Labarai

Karshen Tika Tik : Kotu ta hana Ganduje da hukumar yaki Da Rashawa daukar mataki Akan Sarki Sanusi

Wata babbar kotun tarayya ta hana Gwamna Ganduje da hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano daukar mataki akan Sarki Sanusi

– An bayar da umurnin ne akan rahoton binciken farko da hukumar yaki da rashawar ta ayar kan masarauta inda ta zarge ta da almubazaranci da kudi naira biliyan 3.4

– Justis Obiara A. Egwuatu ya kuma yi umurnin sanar da wadanda ake karat a hanyar wallafa wa a wasu jaridu

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Kano a ranar Talata, 18 ga watan Yuni ta bada umurnin dakatar da gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Ganduje da hukumar dake karban korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar daga yin aiki da rahoton farko dake zargin masarautar kano da almubazaranci da kudi kimanin naira biliyan 3.4.

Umurnin ya biyo bayan wata kara da Muhammad Manir-Sanusi, Dan Buran Kano ya shigar, inda ya bukaci a dakatar da Ganduje da hukumar, da babban alkalin jihar ko jami’ansu daga yin aiki da rahotannin bincike na farko da aka gudanar.

Justis Obiara A. Egwuatu ne ya yane hukucin, inda ya kuma bada umurnin cewa a sanar da wadanda ake karan ta hanyar bugawa a jaridar Daily Trust da kuma babban Lauyan jihar.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: APC ta yanke shawarar korar AbdulAziz Yari da Lawal Shuaibu daga jam’iyyar

An daga sauraran karan zuwa ranar 28 ga watan Yuni don cigaba da shari’a

Hukumar yaki da rashawar a ranar 14 ga watan Yuni ta gabatar da rahoton farko na binciken na zargin da ake yi sksn masarautan Kano ga Sakataren Gwamnatin jihar domin daukar mataki.

®Legithausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button