Labarai

Idan Baku Son Jin Gaskiya Kada Ku Gayyaceni, Inji Sarkin Kano Muhammad Sanusi II

Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi Na Biyu Ya Amsa Gayyatar Zuwa Taron Karawa Juna Ilimi Da Ofishin Babban Akawu Na Kasa Ya Shirya A Gidan Gwamnatin Jihar Kano Kuma Suka Gayyaci Sarki Sunusi.

Sarkin Yayi Jawabi Akan Cigaban Kasa, Tare Da Gargadin Shugaban Kasa Buhari Akan Ya Daina Kashe Makudan Kudade Wajen Abubuwan Da Bana Ilimi, Lafiya Ko Kayan More Rayuwa Ga Jama’a Bane. Sarkin Ya Nuna Damuwarsa A Yadda Gwamnatin Tarayya Ke Kashe Kaso 70% Na Jimillar Kudaden Shigowa Wajen Biyan Bashi, Tare Da Bayyana Cewa Kashe-Kashen Kaso 30% Kacal Na Kudin Shigowar Gwamnati A Ayyukan Inganta Rayuwar Jama’a Bazai Bunkasa Tattalin Arzikin Kowacce Kasa Ba.

Sarki Sunusin Ya Kara Da Cewa “Najeriya Ta Kai Makura A Halin Da Ake Ciki Na Bashin Tirilliyan N24.4 Da Ake Bin Najeriya.” Sarkin Yace Gaskiya Ta Zama Dole Mu Fada Ko Baxa’a Dauka Ba, Sannan Yace “Tunda Kuka Gayyaceni Nan Wajibine Ku Saurari Abinda Zan Fada. Idan Kuma Baku Son Jin Gaskiya Kada Ku Gayyaceni.”

Kadan Daga Jawabin Mai Martaba  Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II CON.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button