Daga karshe: Buhari ya saka baki cikin rikicin Ganduje da Sanusi
Daga karshe, Shuugaba Muhammadu Buhari ya saka baki cikin rikicin da ke faruwa tsakanin gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.
An dade ana kira ga Shugaban kasar da dattijan arewa su sasanta tsakanin gwamnan da Sarki duba da cewa rikicin na daukan sabon salo.
Wata amintaciyar majiya daga fadar shugaban kasa ta shaidawa Daily Nigerian cewa shugaban kasar baya jin dadin abinda ke faruwa a jihar Kano sakamakon korafe-korafe da fargabar tabarbarewar tsaro.
“Ka san cewa shugaban kasa bai cika yin katsalandan a harkokin jihohi ba. Amma kan wannan batun, ya zama dole shugaban kasa ya saka baki,” inji majiyar.
“Shugaban kasa bai ji dadin yadda gwamnan ya rarraba masarautar ba kuma da yunkurin da ya ke yi na tsige sarkin.
“Hakan ya sa shugaban kasan ya kira Ganduje a ranar Alhamis kuma ya umurci Direkta Janar na DSS ya kira taron gaggawa da gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma.
“Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne ya jagorancin gwamnonin bayan ya gana da shugaban kasar ya yi masa bayanni kan halin tsaro a ranar Alhamis. “
Daily Nigerian ta kuma ruwaito cewa shugaban kasar ya kira sarkin zuwa taron gaggawa tare da Madakin Kano, Yusuf Nabahani a ranar Juma’a.
Idan ba a manta a ranar Laraba, Legit.ng ta ruwaito muku cewa Sarki Sanusi ya soke Hawan Nassarawa bisa umurnin Gwamna Ganduje inda ya ce anyi hakan ne saboda dalilan tsaro.