Inda aka kwana a batun sulhunta Gabon da Amal
Tun bayan da wani kwamiti na mutum takwas karkashin jagorancin Malam Khalid Musa da mataimakinsa Sani Sule Katsina da aka dora masa alhakin sasanta jaruma Hadiza Gabon da kuma Amina Amal ya fara zama don sasantawar har zuwa yanzu ba a ji inda batun sulhun ya kwana ba.
A kwananin baya kwamitin ya yi zama hudu da dukkan wadanda abin ya shafa, inda ya fara zamansa na farko ne da lauyoyin Amal, sai na biyu da lauyoyin Gabon, na uku kuma da Gabon, sannan na hudu da Amina Amal.
Aminiya ta gano cewa kwamitin wanda kungiyoyin ’yan fim na Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da kuma Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN) suka kafa ya shirya zaman bai daya da dukkan bangarorin da abin ya shafa a ranar Alhamis din makonni biyu da ta gabata, sai dai a ranar da aka yi zaman Amal ba ta samu halarta ba, kuma tun daga wannan lokaci batun sasantawar ya kwanta.
Aminiya ta gano a yayin zaman karshen jaruma Gabon da lauyoyinta sun halarci zaman, yayin da Amal ba ta samu halarta ba sai dai lauyoyinta.
Idan ba a manta ba dai rikici tsakanin jaruman ya samo asali ne wanda ya yi sanadiyyar da masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood ta samu kanta cikin rudani dalilin dora wani hoton tsiraici da jaruma Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina Amal ta yi a shafin sada zumunta na Instagram.
A hoton jarumar ta sanya matsattsun tufafin da suka fitar da surarta har da cibiyarta a waje, hakan ya sanya mutane suka yi alla-wadai da abin da ta yi, inda a ciki har da ’yan fim da suka hada da Hadiza Gabon da A’isha Aliyu Tsamiya da Hassan Giggs da Baballe Hayatu da sauransu.
A karkashin hoton da Amal ta sanya din ne Gabon ta rubuta ba da haka Amal za ta yi suna ba, inda A’isha Tsamiya ta ce abin da Amal ta yi ne yake sa a rika zagin Kannywood.
Daga baya kuma Amal ta sake sanya wani hoto a shafinta na Instagram mai dauke da wata hira, inda a karkashin hoton ta rubuta sai dai a kira ta karuwa saboda shigar tsiraici da ta yi, amma ita ba ta madigo, al’amarin da ya fusata Gabon har ta kai daukar wani mataki da a karshe ya sa aka maka ta a kotu, sannan wadansu lauyoyi 12 suka tsaya wa Amal.
Sai dai a yayin da yake tattaunawa da Aminiya daya daga cikin mamban kwamitin sasancin, Malam Salisu Mohammed Ofisa, wanda kuma shi ne Sakataren kungiyar MOPPAN ta Jihar Kano, ya bayyana cewa, a yanzu lauyoyin Amal sun dan taka wa kes din burki, har sai sun ga yadda kwamitinsu ya gama taka rawa wajen sulhun.
Ofisa ya ce abin da lauyoyin Amal suka yi abin a yaba ne, kuma sun nuna a shirye suke don ganin an yi sulhun.
Ofisa ya ce an ji shiru dangane da batun sulhun ne saboda Amal ta tafi Saudiyya aikin umrah, amma da zarar ta dawo za a ci gaba zaman sulhun.
Ya ce, “Ita Amal a yanzu ba ma ta nan, ta je Saudiyya, amma muna ta magana da lauyoyinta, kuma ka ga mai kara dole sai yana nan za a yi sasanci. Amma tun da ba a shiga kotu har yanzu ba, to a kan maslaha muke.”
Ya kara da cewa a zaman da aka yi na karshe lauyoyin Amal sun bukaci Hadiza Gabon ta ba Amal Naira miliyan 10.
“A gaskiya (lauyoyin) sun ce za a janye kes amma akwai abin da suke so, inda suka zo mana da kasafin Naira miliyan 12, a gaskiya mun kalli abin mun ga ba zai yiwu a cimma shi ba, sun nemi a ba su Naira miliyan 12, sun kuma ce sun bukaci hakan ne saboda sun yi abubuwa a kotu da kuma batun dameji, sannan kuma sun bukaci Gabon ta je gidajen rediyo ta ba Amal hakuri.” Inji Ofisa.
Sun ce lauyoyin sun fadi hakan ne kawai a matsayin tayi, “haka din kamar matashiya ce, amma za su ga abin da za mu iya yi a kai, ba wai sun ba Gabon ne kasafin ba ne, kungiya suka ba, ita kuma kungiya ina ta ga irin wannan kudi, kungiya sulhu take so.”
Ya ce,“Ko da Amal tana Saudiyya za mu ci gaba da magana, amma dai a yanzu abubuwa sun tsaya dai a bangarenmu na shugabanci, amma dai har yanzu ba a sa ranar sauraren kara a kotu ba, sannan lauyoyin Amal sun yi mana alkawari za su ja kafa har a kai ga samun maslaha” inji Ofisa.
Ibrahim Birniwa wanda shi ne Manaja kuma mai magana da yawun jaruma Hadiza Gabon ya bayyana cewa sun saurari hirar da Amal ta yi a gidan rediyo a Kano, sun kuma karanta hirar da ta yi da jaridar Daily Trust, amma jarumar ba za ta ce komai a kan zarge-zargen ba, don gudun kada a kara jan magana, domin sulhu ake bukatar a yi, ba wai sake rura wutar rikici ba.
Ya ce, “Mun je an yi zama na farko, amma Amal ba ta zo ba, amma dai an fahimci juna tsakaninmu da lauyoyinta, sai aka sa wata rana da ya kamata Amal ta zo, sai dai lauyoyinta ne suka zo, ita ma Hadiza ta zo da nata lauyoyin,
“An fafata tsakanin lauyoyin bangarorin biyu, lauyoyin Amal sun nemi a ba da Naira miliyan 10, shi ne kungiya ta ce musu hakan ba mai yiwu ba ne, inda daya daga cikin lauyoyin Amal ya ce sun bukaci a ba da Naira miliyan 10 din a matsayin tayi, ba kuma lallai dole Naira miliyan 10 za a bayar ba, daga nan lauyoyin Hadiza suka ce in dai sulhu ake so a yi, to a zauna a yi sulhun.”
Ya ce, “Da yawa daga cikin zarge-zargen da Amal ta yi ba su da makama, kuma in an ci gaba da jan magana, abu ne da za su haifar da tababa, saboda haka babu abin da ya fi dacewa a zauna a yi face sulhu din, don maganar ta wuce.”
Sources:aminiya