Labarai

Yan Najeriya sun gasu a mulkin Buhari – Omotola

Mashahuriyar tsohuwar ’yar fim din Nollywood, wadda ta dade ana damawa da ita, Omotola Jegede-Ekeinde, ta bayyana irin rayuwar kuncin da ‘yan Najeriya ke sha a lokacin wannan mulkin na Shugaba Muhammadu Buhari.
Omotola ta ce radadin kuncin da ake sha kamar “zafin wuta” ya ke. Haka ta bayyana irin matsanancin halin da ta ce ake ciki, a shafin ta na twitter.
Omotola mai shekaru 41 a duniya, ta kara watsa wannan koke da ta yi a shafin ta na Instagram.
Dukkan sakonnin na ta dai sun dauki hankalin jama’a da dama a twitter da kuma Instagram a jiya Lahadi bayan ta watsa bayanan.
“Haba Buhari! Kasar a kan idon ka ana rayuwa cikin zafin kunci kamar “zafin wuta!” Haka ta bayyana kuma ta yi adireshin soshiyal midiya ta tura a shafukan @ProfOsinbajo @MBuhari @NGRPresident.
Ta kuma roki Buhari da Osinbajo su gaggauta kamo bakin zaren da hanzari.
Omotola ta yi bayani ne dangane da yawan kashe-kashe da ake yi a fadinn kasar nan ba wani dalili.
Ta ci gaba da cewa: “Jama’a na fama da bakin talauci da mummunar fatarar rashin kudi, ga kuma ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da jami’an tsaro ke yi. Wannan ai sai ya tarwatsa kasar! Abin ya wuce yadda mutane za su iya daurewa fa!” Inji Omotola
Omotola, wadda ‘yar rajin Kungiyar Jinkai ta Duniya, Amnesty International ce, kwanan nan ne kuma ta yi kira da a sa dokar-ta-baci a Zamfara da jihohin da ake fama da akashe-kashe.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button