Sharhin Fim Din Mijin ‘Yayata’
Suna: Mijin Yayata
Tsara Labari: Nura Mustafa Waye
Kamfani: Intishar Multimedia
Shiryawa: Rabi’u The King
Umarni: Nura Mustafa Waye
Jarumai: Ali Nuhu, Jamila Nagudu, Isa Adam, Fati Shu’uma, Rahma M.K, Bilkisu Shema, Xanta Bashir, Baffa Baffancy, Jazuli Kazaza, Maryam Qosawa. Da sauran su.
Sharhi: Hamza Gambo Umar
A farkon fim din an nuna Kabir (Ali Nuhu) ya kira wayar matar sa Maryam (Jamila Nagudu) ya shaida mata cewar yana jiran Sadiya kanwarta a waje.
Sadiya (Fati Shu’uma) budurwa ce wadda ke zaune a gidan yayarta Maryam kuma tana karatun jami’a, a kullum Kabir ne yake kaita makaranta sai dai kuma kafin su fara zuwa makarantar sukan fara biyawa ta wani wajen, a wasu lokutan ma ko Sadiya ta baro gida ba makarantar take tafiya ba, hakan ne kuma ya soma damun saurayin ta Nura (Isah Adam) nan ya soma korafi akan karfin alakar Sadiya fa Kabir mijin yayarta Maryam, sai dai kuma ita Sadiyar tana kokarin boye masa abinda ke faruwa tsakanin ta da mijin yayarta.
Yayin da a bangare daya kuma Zainab (Bilkisu Shema) suke soyayya da nata saurayin wanda ita kuma damuwar da take ciki bata boyuwa a fuskar ta ko da a makaranta ne, domin ta kasa mancewa da cin amanar da mijin mahaifiyar ta yayi mata (Jazuli Kazaza) hakan yasa ko ta dawo daga makaranta bata gaishe sa, yayinda mahaifiyar ta Amina (Rahma M.K) abin yake damunta har ta soma zargin ko wani abu ne ya faru tsakanin su, sai dai kuma duk irin tambayar da tayiwa ‘yarta Zainab amma bata fada mata komai ba.
Haka a bangaren Salma mu’amular su tayi karfi sosai da mijin yayarta Kabir, sanadin hakan yasa zauntuka suka soma yawa har Maryam ta samu labarin ana yawan ganin kanwarta da mijin ta a asibiti. Jin hakan ne yasa zargin ta ya soma hawa kan su, wanda sanadin hakan ne ma ta sanya idanu sosai akan kanwarta, ai kuwa kwatsam sai ta kama ta suna waya da mijinta Kabir wanda kuma ba magana ce da ta dace ba, tun daga wannan lokacin ta nunawa kanwarta Salma cewar ta san komai.
Maryam tayi yunkurin barin gidan mijinta saboda zargin shi da kanwar ta sun ci amanar ta, amma sai Kabir ya dakatar da ita gami da gaya mata gaskiyar cewa ba abinda take zargi bane ke faruwa a tsakanin su, domin Salma ta taba sanar masa da tana da juna biyu amma bata sanar dashi wanda yayi mata ba, dalilin hakan suke zuwa asibiti saboda likita ya nuna akwai wata matsalar a cikin nata.
Jin hakan ne yasa Maryam ta fahimci ba abinda take zargi bane ke faruwa tsakanin kanwar ta da mijinta Kabir, a sannan ne Salma ta basu labarin cewar mahaifin Zainab ne yayi mata fyade a dalilin zuwan ta gidan su Zainab din bayan ya saka mata maganin bacci a lemo, jin hakan ne yasa Kabir yasa aka kama mahaifin Zainab wanda shima anan ya tabbatar musu da bashi yayi fyaden ba wasu ‘yan isakn makaranta ne da suka tilasta shi nemo musu Salma.
Da aka tsaurara bincike ne aka gane cewar da sa hannun Nura saurayin Salma hasalima shi yayi mata fyaden da ta samu ciki. Jin hakan ne yasa Salma ta suma yayin da a karshe juna biyun jikinta ya zube, har ta soma tunanin babu namijin da zai aure ta sai Maryam yayar ta ta tabbatar mata da cewar mijinta Kabir zai aure ta. Anan ne Maryam ta bada labarin cewar Salma ba ciki daya suka fito ba ‘yar kanin mahaifinta ce. Yayin da a fannin Kabir shima ya amince da zai auri Salma.
Abubuwan Birgewa:
1- labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa, kuma har fim din ya kare labarin bai karye ba.
2- Hoto ya fita radau, sauti ma ba laifi, haka kuma an yi amfani da salon daukar hoto me tsari.
3- Sunan fim din ya dace da labarin, wato “Mijin Yayata”
4- Kalaman bakin jaruman sun yi dadi gami da ma’ana, wato “Dialogue”
Kurakurai:
1- Makarantar da aka nuna su Salma suna karatu a matsayin jami’a kai tsaye tafi kama da wajen kiwon namun daji wato gidan zoo, musamman idan akayi la’akari da manyan keji irin na tsare dabbobin dawa, tare da danbareren hotan giwa wanda duk aka nuna a cikin makarantar.
2- Shin ina iyayen Salma ne? Haka kuma wane sanadin ne yasa Salma (Fati Shu’uma) ta dawo gidan yayarta da zama? Shin iyayen nasu mutuwa sukayi ne da har rukon Salma ya dawo hannun yayar ta Maryam ko kuma taya yayar ta? Ya dace a bayyana dalilin zaman ta a gidan yayar ta koda ta hanyar nuna cewar iyayen su ba ‘yan garin bane ita kuma karatun jami’a ya kawota gidan yarta.
3- Lokacin da ake dukan su Garbati a ofishin ‘yan sanda, wato ‘yan daban makaranta wadanda ake tuhumar su don su fadi wanda ya yiwa Salma fyade, jami’an tsaron da aka nuna suna dukan su yanayin su sam basuyi kama da jami’an tsaro ba, don sun fi kama da ‘yan bangar siyasa, saboda ko uniform din ‘yan sanda babu a jikin su balantana hakan ya boye wata siffar su mara kyawu.
4- Hujjar da Kabir ya bayar (Ali Nuhu) wadda ta sa su Maryam suka gamsu da cewar Nura ne ya yiwa Salma fyade, sam hujjar ba ta da karfi ko kuma gamsarwar daya dace a yarda da maganar shi, Domin ba’a nuna cewar yasan Nura da wata dabi’a mara kyawu ko kuma ya gansa a lokacin da duk ya shirya makircin yiwa Salma fyade ba, haka kuma babu wani labari da ya samu akan Nura wanda hakan zai sa ya sanar da cewar Nura ne yayi fyaden ba. Ya dace a samar da kwakwkwaran dalilin da mai kallo zai gamsu da cewar an gane cewar Nura ne ya yiwa Salma fyade.
5- Shin mecece makomar Nura ne? (Isa Adam) duk da an nunawa me kallo cewar an gane Nura ne ya yiwa Salma fyade kuma har ta samu juna biyu, amma ko a baki ba’a fadi wani hukunci ko mataki da aka dauka a kansa ba.
Qarkarewa:
Labarin yayi nasarar rike me kallo har zuwa inda ake son nuna masa wani sako, kuma labarin ya fadakar domin an nuna illar zargi da rashin bincike tare da illar cin amana wanda hakan yakan haifar da matsala a cikin al’umma. Sai dai kuma duk da haka akwai abubuwan da ba’a karkare ba, tare da wasu abubuwan da ya dace a kara inganta su. Wallahu a’alamu!