Labarai
Fatima Ganduje Ta cacacaki Masu Sukar Mahaifinta A twitter
Diyar gwamnan Kano kuma surukar gwamnan Oyo mai barin gado Fatima Ganduje, ta yi amfani da shafin Twitter inda ta caccaki masu sukar mahaifinta.
Fatima a cikin wasu tweet da ta yi ta bukaci duk mai korafi ya yi ta laluma, daga baya sai ta ce to yanzu za ta mai da martani.
A cikin wasu rubutun nata ta yi shagube ga ‘yan jam’iyyar PDP da jigon jam’iyyar PDP a Kano, Rabi’u Musa kwankwaso.
An dai shafe tsawon lokaci ba a ji duriyar Fatima Ganduje a shafukan sada zumunta ba, musamman a lokutan yakin neman zabe da kuma zaben gwamnoni da aka yi ranar 9 ga watan Maris, inda a lokacin sakamako ya nuna Abba K Yusuf na PDP ya yi wa mahaifinta fintinkau da fiye da kuri’a 26,000.
Sai dai jim kadan bayan gudanar da karshen zaben gwamnan jihar Kano din, inda hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta ayyana mahaifinta a matsayin wanda ya lashe zaben, sai aka fara ganin sakonnin Fatima a shafukan sada zumuntar, inda take warkajaminta da taya mahifinta murnar nasarar da ya samu.
Fatima ta ce a baya lokacin da mutane suka yi ta maganganu lokacin aurenta da dan gwamnan Oyo Idris Ajimobi, ta ki mayar da martani ne saboda “hutun auren da ta dauka ya yi matukar dadin da ba ta da lokacin mai da martani kan komai.”
Shagube ga Kwankwaso
A cikin wani rubutun nata tace “ya kamata ka cire wannan mukamin na Injiniya da kake sanya wa kanka.” Sai dai duk da ba ta ambaci suna ba, mabiyanta sun dau haske cewa ga dukkan alamu da Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso take.
A wannan rubutun kuma na kasa Fatima ta yi tsokaci ne kan wani hoto da ke nuna mahafinta da Jagaban na Jam’iyyar APC wato Bola Ahmed Tinubu, inda suke maganar da ba a san ko ta mece ce ba, amma sai ma’abota Twitter suka yi rubutu kamar haka:
@GovUmarGanduje: Nagode Asiwaju por ya suffort, Walai .. Zha election .. Eez nor eazy
@AsiwajuTinubu: No Shaking !!!
Wato Ganduje na cewa cikin turancin da aka fi danganta shi da Bahaushe: “Asiwaju na gode da goyon bayanka, Wallahi mun sha wuya a zaben.” Shi kuma Asiwaju ya amsa da cewa: Kar ka damu ba matsala.”
To sai dai wannan hoto da Fatima Ganduje ta sa zai iya bai wa mutane mamaki, ganin irin salon turancin da aka danganta babanta da shi, yawanci ‘yan kudu ke tsokanar ‘yan arewa da shi.
Sannan kuma ba a san ko me ya sa ta danganta nasarar baban nata da kokarin Bola Tinuba ba, ganin cewa dama an yi ta zargin su Tinubun da zuwa Kano don murde zaben cike gurbin da aka yi don gudun kar jam’iyyarsu ta APC ta fadi.
Rawar Goggo
A wannan sakon na kasa kuma, wani ne ya wallafa rawar da matar Ganduje kuma mahaifiyar Fatima ta yi a lokacin yakin neman zabe a Kano, yana mai yi wa iyalan Gandujen ba’a da cewa “Ku kam title dinku ay ya fi na kowa muni ko a Italia za’a dade ba asami mai abin kunya irin naku ba.”
Ita kuwa Fatima sai ta ba da amsa da alamar dariya tana cewa: “Yawwa guggan karfe, ko mai takalmin karfe ya barki, kalli yadda take rawa yadda na nuna mata, macen da ke birge ni kenan.!”
Ga dai karin wasu rubuce-rubucen da Fatima Ganduje ta wallafa a Twitter
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Leave Comment Here