Uncategorized

Sirrin Rike Mijinki Amarya

Yana da kyau mace ta san hanyoyin burgewa da jan hankali wanda zata yi ta dauke hankalin mijin ta daga sauran mata. Yana daga cikin dalilan aure fa, rintsewa miji ganin sa kamar yadda Manzon Allah (SAW) yace:
“ya ku taron matasa, duk wanda ya samu dama to yayi aure, domin shi ne zai fi rintse masa ganin sa, kuma zai fi kiyaye masa farjin sa……). Yar uwa kin ji amfanin ki shine ki rintse masa ganin sa, ki hana shi kallon matan da basu dace ya kalla ba, a kan titi. In har ba ki iya cika wannan aikin naki ba, to menene amfanin auren naki? Wadannan hanyoyi suna da yawa sosai, amma ga kadan daga cikin su:

Kwalliya:
Wasu matan basa yin kwalliya sai in zasu tafi biki. A kasar hausa, zaka samu gidan da in yaro yaga uwar shi tana goge kafa ko kuma wani abu sabo na kwalliya sai kaji yana cewa “nima zan je”, ba tare da an ce masa tafiya za’a yi ba. Ya kamata mace ta zamto mai kwalliya domin da haka aka san ta. A lokacin da mushrikan Makka suka jingina ‘ya’ya mata ga Allah sai Allah ya ce “Yanzu wacce aka rene ta akan kwalliya……..” (Surah Zukhruf 43:18). To mata kun ji asalin ku.
Haka kuma, hausawa sun ce “ba’a mace mummuna”. Haka zancen yake. Wani mutum yana da matar sa mai kyau amma bai san tana da kyau kamar yadda take ba, sai yayi mata kishiya saboda bata gyara jikin ta, bata kwalliya. Sai da aka kawo amarya, sai wata rana mai gida ya shigo gida sai ya samu amaryar sa da matar sa ta farko a kan kujera, a lokacin ya fahinci ashe ta farkon ta fi amaryar kyau. Kin ga wannan ita ta jawo aka yi mata kishiya, kuma kema in kika zama irin ta, to tabbas ko mai gidan ki bai shirya ba zai kara aure.

Kwalliya ta hada da iya saka kaya, iya daura zani, kar ki rinka yin daurin zani yayi bakin kaza, iya daurin dankwali, hajiya ki koyi dauri kala kala ta yadda sai ayi kwana goma kullum daurin da zaki yi daban. Kafin a zagayo har ya manta da wani, sai ki dauwama a matsayin amarya. Ki kasance mai sanya turare, mai gyara gashi da kitso na zamani, kala-kala, da kunshi, musamman na zamani dan yayi.
Iya tafiya
Dole ne mace ta iya tafiyar jan hankali. Ki iya yanga da jan aji. Kar ki rinka tafiya kamar kura ta hango nama a daji, kina tafiya buguzum-buguzum kina ta da kura. Hakan zai sa mai ran mai gida ya sosu kuma ke ma kayan ki zai yi datti da wuri. Haka nan, kurar da take tashi zata iya shiga jikin ki, musamman gaban ki, ta jawo miki matsala.

Kalaman soyayya
Wasu matan basu iya kalaman soyayya ba. Wassu kuma kunya suke ji su yi wa mazajen nasu irin wannan kalaman! Ita kawai tunanin ta, idon an yi aure to babu maganar soayayya! Hajiya kin kashe kan ki! Ai ko bayan shekara nawa ne da aure, akawai maganar soyayya, kuma ko ‘ya’ya nawa kika haifa. Yanzu abun mamaki ne don ‘yar shekara arba’in ta fito tana cewa mijin ta: “haba masoyi na”, “haba mizirarin soyayyar zuciya ta”, “ya wanda in ban gan shi ba bana iya barci”? ko kadan. Haka ake so wacce ta fi shekara arba’in ma tayi, amma wai sai kaga ‘yar shekara 25 zuwa 30 tana jin kunyar fada! To kuwa wata zata fada masa a waje kuma ya shigo miki da ita gida, kuma ba yanda zaki yi da ita.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA