Labarai
SHUGABA BUHARI ZAI KAFA TARIHI Za A Yi Bikin Kaddamar Da Rijiyoyin Man Fetur Da Aka Samu A Jihar Bauchi
Daga Datti Assalafiy
Hukumar kula da albarkatun man fetur na ‘kasa (NNPC) ta fitar da sanarwan cewa gobe Asabar 2-2-2019 shugaba Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin rijiyoyin men fetur da aka samu nasaran tonawa a yankin kogin Kolmani dake karamar hukumar Alkaleri jihar Bauchi.
Wannan shine karon farko a tarihin duniya da aka yi nasarar tona rijiyoyin man fetur a arewa kuma a karkashin gwamnatin shugaban ‘kasa Muhammadu Buhari, sannan jihar Bauchi za ta shiga jerin jihohi masu arzikin man fetur a Nijeriya.
Wannan nasara ce daga Allah, Baba Buhari mun gode, Allah Ka taimaki shugaba Buhari Ka kara masa taimako da nasara. Amin.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com