Ni Ba Soyayyar Kudi Nake Yi Wa Buhari Ba, Soyayya Ta Tsakani Da Allah Nake Yi Masa, Cewar Aminu Saira
Daga Aliyu Ahmad
Fitaccen Darktan nan na finafinan Hausa, Malam Aminu Saira, ya bayyana cewa shi ba dan siyasa ba ne kuma ba shi da jam’iyya, kawai shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.
Fasihin Daraktan, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da Editan RARIYA ta wayar tarho. Inda ya kara da cewa babu ruwansa da wasu sabgogin ‘yan siyasa, amma yana tare da shugaba Buhari dari bisa dari.
“Duk dan Arewa mai hankali da tunani ya san irin nawuyacin halin da wasu daga cikin jihohin Arewa suka tsinci kansu a ciki kafin zuwan shugaba Buhari. Ko mu nan a Kano muna sane da hakan. Don haka ko iya wannan hujja ya isa na so Buhari saboda zaman lafiya da aka samu”, cewar Malam Aminu Saira.
Malam Aminu Saira ya kara da cewa iya rufin asiri da daukaka Allah ya huwace masa, don haka ba kudi yake bukata kafin ya so Buhari ba, kawai soyayya ce ta tsakani da Allah yake yi masa.
Malam Aminu Saira shine ya bada umarni a manyan finafinan Hausa irin su Dan Marayan Zaki, Garinmu Da Zafi, Ga Duhu Ga Haske, Jamila Da Jamilu, Balaraba, ‘Ya Daga Allah, Jidda, Walijam da sauransu da dama.