Mata Ku Bani Hankalin Ku A Nan
MATA KU BANI HANKALIN KU ANAN,KU NUTSU TAMKAR KUNA KARANTA LITTATTAFAN SOYAYYA DA SHAQUWA. Yar uwa lokaci yayi da ya kamata mu nutsu mu san me mukeyi mu kyautata duniyar mu da lahirar mu mu samu rabauta a ranar gobe kiyama. Yan uwana mata mu kula sosai da samarin mu wanda sukazo da wanda zasu zo,soyayya fa ba hauka bane,ya kamata mu gane. ——yar uwa ki lura da kyau ki gane namiji fa duk abunda zai yi ado ne a wajen shi me yasa zaki bari ya rudi zuciyar ki har ku kai ga aikata iskanci.mtswww ke kuwa baiwar Allah me yai miki zafi?me yasa bazaki jira ranar da zaki zama halalinshi ba?ranar da kowa da kowa yake murnar zaki tafi gidan ki na sunna?ranar da baki da fargabar ace wani ya ganku a daki?ranar da zaku raqashe ku ci karen ku ba babbaka?yar uwa ki rabu da yan iskan samarin da zasu rude ki,ki sani idan saurayi ya kai ki daki zaku kasance cikin fargaba da tsoro duka duka abinda zakuyi bazaku wuce minti 10 ba cikin tsoro………to ki gane kunyi minti goma dashi ya jawo miki zaman gidan shekara goma sai dai in Allah ne ya yanke mk wahala. Yar uwa ta na tabbatar kowacce mace tasan abinda namiji zai fara yi ta gane dan iska ne.to ga shawara Daga lokacin da kka fahimci ya zo miki da haka ci ubanshi,daga mishi red card,ki shafe shege ki manta da rayuwarshi wallahi za ki samu canji mafi alkhairi……. ……… Mata mu gane mu ba a duniyar marubuta muke ba da uncle wane ko yaya wane ko doctor wane zai tatta6eki,rungumeki,tsatstsotseki,lallatsaki,da lallashe ki ba tare da aure ba wai nan soyayya ce kuma ki kwana lafiya,ki tina duniyar gaskiya muke wacce ayyukan mu su zasu zama guzurin mu na gobe qiyama. Yar uwa kema ya zama dole ki kasance mai kiyaye abinda zai ja aikata 6arna,ki sani ke ba wance beauty bace kamar a littafi da zaki tsuke jiki ki saki gashi ki zo gaban saurayi ko bare ko dan gida,ubangijinmu ya haramta hakan.wallahi fidda tsaraicinki ba zai qara wa namiji sonki na gaskiya ba sai dai qara motsa sha’awarshi akan ya kusance ki wanda hakan shi ke kawo aikata zina kafin aure. kada ki sake ki bada kanki bore ya hau kada ki zama mai rauni har wani bunsuru ya samu galaba a kanki domin da zarar kin amince kin zama tinkiya kada ki sake ki tayashi furta maganar batsa ga junan ku kada ki sake ya kaiki wani daki ko wani waje yace ki tayashi hira kada ki nuna mishi wani sashe na jikin ki domin shi namiji kwadayayye ne. Mata mu kiyaye mu hankalta mu kare mutuncin mu da na zuriar mu. WANI ABUN LURA *duk iyaye suna buqatar ‘yarsu ko dansu ya zama na gari.mu basu mana *duk wani namiji yana neman mata ta gari.mu zama na gari *duk wata uwa tana buqatar danta ya auri mace mai nagarta.sai fa mun gujewa sa6on Allah *duk wata mace burinta ta zama yar lelen mijinta.ki shiga da mutuncin ki. Mata ina dada kira a gareku duk abinda muka aikata qarshe kanmu yake komawa. ZO KIJI Da zarar kin dau ciki yan gidanku zasu guje ki iyayen ki zasuyi Allah wadai da haihuwarki yan unguwa zasu samu topic,shi kuwa fa?yan gidansu zasu ce kayi wauta shikenan ta wuce iyayenshi zasu ce qarya ne dansu bazai aikata ba abokanshi zasuce aboki kayi aiki.nayi qarya?hmmmm ko ma dai menene………… Wlh ko da zaki kaishi duk kafafan yada labarai kina bayyana illar da yai miki babu abinda zai hanashi samun mace.idan zaki yada yau muddin yaso aure kafin ranar ta zagayo zakiji maganar bikinshi ta yadu ke kikai iskanci shi ado yayi. Ke kuwa baiwar Allah wallahi qanwar ki da ba a haifa ba sai tayi aure ta barki don babu wanda zai kwashi jagwal. To idan har haka ne lallai ya zama dole mu hankalta mu dawo hankalinmu mu gujewa samarin iska ba birgewa bace kuma ba wayewa bace. A qarshe ina qara nusar damu mata mu sani Allah yayi mana dinbin daraja wanda idn muka kiyaye zamu more ta.
DON ALLAH INA KIRA GA DUK WANDA YA SAMU SAQON NAN YA TURA GA YAN UWA MATA DOMIN MU AMFANA,KADA A MANTA MANZO SAW YACE MUYI QOQARIN KAWAD DA MUMMUNA DA HANNUNMU IDN BAZAMU IYA BA DA HARSHENMU……….HAR DAI ZUWA QARSHEN HADISIN,YANDA NAYI AMFANI DA HANNU NA WAJEN TYPING NA ISAR DA SAQO NA ROQEKI/KU DA KU/KI YI AMFANI DA HANNUNKI WAJEN YIN FORWARDING WANNAN SAQO,ALLAH KADAI YASAN INDA ZAIJE DA KUMA WANDA ZASU AMFANA. NAGODE DA BANI LOKACI WAJEN KARATU ALLAH YA SAKA MIKI DA ALKHAIRI ALLAH YA DADE TSARE ZUKATANMU DAGA AIKIN SHAIDAN ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR MU ALLAH KUMA YA SADAMU DA MAZAJE NA GARI…… Names of spices in Hausa – English. I find this particularly useful. If you know some more, pls keep updating and sharing back for our collective benefit. Names of spices in Hausa – English 1.Cloves – kanumfari
2. Fenugreek – Hulba
3. Scent leaf – Doddoya
4. Cinnamon – Kirfa
5. Potash – Kanwa
6. Mint leaf – Na’a na’a
7. Pumpkin – Kabewa
8. Bitter leaf – Shuwaka
9. Spring onions – Albasa mai lawashi
10. Sesame – Ridi
11. Tamarind – Tsamiya
12. Jute leaf – Rama
13. Garlic – Tafarnuwa
14. Nutmeg – Gyadar Kamshi
15. Ginger – Citta
16. Moringa – Zogale
17. Turmeric – Kurkur
18. Locust Beans – Daddawa
19. Chilli – Shambo
20. Egg plant leaf – Ganyen Gauta
21. Cress – Lansir
22. Honey Locust – Dorawa
23. Baobab Leaf – Kuka
24. Jujube Powder – Garin Magarya
25. Spinach – Alayyahu