Labarai

Yanzu-yanzu: Bayan kwanaki takwas, Yan sanda sun damke Dino Melaye

Bayan kwanaki takwas da zaman din-din-din da jami’an yan sanda sukayi a kofar gidan dan majalisar dattawan Najeriya mai wakilta Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye, ya mika wuya ga hukuma. Mun samu rahoton daga jaridar BBC cewa Dino Melaye a ya mika wuya ne bayan babban kotun tarayya dake zaune a Abuja tayi watsi da karar da ya shiga kotun na bukatan a harmatawa yan sanda kamashi. Jaridar SaharaReporters ta samu labarin cewa Sanata Dino Melaye tare da wasu sanatoci da yan majalisan wakilai sun tafi ofishin sifeto janar domin ganawa da shi amma basu sameshi a ofis ba, kawai sai suka mika shi ga jami’an hukumar.

Mun kawo muku rahoton cewa babban kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta yi watsi da takardar karar da sanata Dino Melaye ya shigar cewa yan sanda su bar kofar gidansa kuma kada ku kamashi. Dini Melaye ya kai kara kotu ne bayan jami’an hukumar yan sanda sun kai masa hari gida a makon da ya gabata kuma har yanzu ya ki fitowa. A shari’ar da Alkalin ya yanke da safiyar Alhamis, Jastis N.E Maha, ya yi watsi da bukatar Melaye amma yace idan yanada kwakkwaran hujja ya gabatar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button