Sports

Real Madrid, PSG Da Barcelona Suna Zawarcin Salah

Wasu rahotanni daga kasar Birtaniya na cewa, manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Barcelona da PSG da kuma Real Madrid, na sha’awar daukar dan wasan gaba na Liberpool wato, Mohamed Salah dan asalin kasar Masar.
Rahotannin na cewa, manyan kungiyoyin sun shirya ajiye zunzurutun kudi fam miliyan 200 a matsayin farashin Salah mai shekaeru 25 kuma tsohon dan wasan Chelsea da kungiyar kwallon kafa ta Roma.
Tauraron dan wasan na Masar na matukar haskawa a ‘yan kwanakin nan, in da ya zura kwallaye da dama a kakar gasar firimiyar Ingila ta bana kuma shine ya lashe kyauta dan wasan dayafi zura kwallo a raga.
Real Madrid dai tanason Salah, wanda baya kokari a wannan kakar sosai ya maye mata gurbin Ronaldo wanda yabar kungiyar zuwa Juventus a watan Agustan daya gabata akan kudi fam miliyan 105.
Sai dai ana ganin mawuyaci ne Liberpool ta sallama dan wasan ga wata kungiya, lura da cewa tana hararar lashe kofin firmiyar Ingila a wannan kakar, kuma rashin Salah ka iya zama barazana a gare ta.
Har ila yau kungiyar ta Liberpool batason siyar da dan wasan nata sakamakon yanzu itace take jan ragamar gasar ta firimiya da maki bakawi kuma an bhuga wasa na 20 a gasar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button