Labarai

Obasanjo: ‘Ko Najeriya ka sace babu komai in kana APC’

A wata hira ta musamman da sashen Yarbanci na BBC, tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya magantu a kan tsohon mataimakinsa wanda a yanzu dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, da kuma a kan Boko Haram da kuma hukumar zabe ta kasa.
Obasanjo ya bayyana cewa ya yi imani cewa shugaban kasa Buhari ya fi Atiku lalacewa, kuma ya bayyana dalilin da ya sanya bai goyi bayan daya daga cikin matasa 73 da ke neman shugabancin Najeriya ba.
A karon farko, ya bayyana abin da faru kafin sojojin Najeriya suka aikata abin da ya zama kisan kiyashi a Odi a shekarar 1999, wanda sojoji bisa umurninsa suka kashe kimanin mutum 2,500 mazauna wani kauye.
Ku saurari fitar cikakkiyar hirar a kan shafukan BBC da karfe 6 na yammacin ranar Talata 22 ga watan Janairun 2019.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.comMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button