Kannywood

Maganar Gaskiya Akan cewa An Kone min Gida – Inji Nura M Inuwa

Godiya ta tabbata ga Allah (SWT) da yasa muka shigo sabuwar shekara lapiya,Allah ya sada mu da alkhairan dake cikinta kuma Allah ya tsaremu da sharrukan dake cikinta ameen.Zanso nayi amfani da wannan damar nayi godiya ga masoya masu yi mana fatan alkhairi,kuma na kara kwantar musu da hankali akan maganganun da ake yadawa wadanda ba gaskiya bane.Sannan ina kara sanar da jama’a cewa Nura M Inuwa da iyalinsa suna nan cikin koshin lapiya da kwanciyar hankali.Bayan haka kuma zanso na kara wayar da kan mutanen da basu sani ba su gane cewa duk cikakken dan kasa yana da ‘yancin zabe ko ya tsaya a zabeshi (Democracy), sannan duk wanda yake sana’a yana da ‘yancin cinikayya da duk wanda yake so kuma a  lokacin da yake so.Dan haka mu dai a koda yaushe fatanmu kasarmu Nigeria ta samu cigaba,Kuma addu’armu Allah ya bamu shugabanni na gari masu kishi da tausaya mana.Ameen. @nura_m_inuwa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA