Uncategorized

Jerin sunayen DIG da zasu yi ritayar dole bayan nada kaninsu a mtsayin IGP

Tun a yammacin jiya, Litinin, ne kafafen yada labarai da dama da suka hada da legit.ng suka wallafa rahoton cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sunan Abubakar Adamu Mohammed a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa. A yau, Talata, kuma shugaba Buhari ya nada Mohammed tare da tabbatar da shi matsayin shugaban rundunar ‘yan sanda na kasa mai cikakken iko, hakan na nufin cewar sai a yau ne ya tabbata IGP a hukumance. Nadin Mohammed a matsayin IGP zai tilasta manyan mataimakan shugaban rundunar ‘yan sanda (DIG) da yawa murabus kamar yadda ta faru bayan shugaba Buhari ya nada Idris a matsayin IGP a shekarar 2016.
Daga cikin manyan mataimakan da nadin sabon IGP zai saka barin aiki akwai; Maigari Abbati Dikko mai rike da bangaren gudanarwa da harkar kudi (FDC), Habila Joshak mai rike da bangaren atisaye, da Emmanuel T. Inyang mai rike da bangaren fasahar sadarwar zamani (ICT).
Kafin amincewa da sunansa a matsayin sabon shugaban rundunar ‘yan sanda, Mohammed, dan asalin jihar Nasarawa, ya kasance mataimaki ga Sifeton rundunar ‘yan sanda. Abokansa na aiki na kiransa da Adamu Lafiya, domin alakanta shi da mahaifar sa, wato babban birnin jihar Nasarawa. 
An haifi Mista Mohammed a ranar 9 Nuwamba na shekarar 1961. Ya shiga aikin dan soja a shekarar 1986 da takardar kammala karatun digiri a Geography. Ya rike mukamin darektan aiyukan jami’an ‘yan sanda a kasashen ketare, tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne a jihar Enugu kafin daga bisani ya zama mataimakin shugaban rundunar ‘yan sanda mai kula da rukuni na 5.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button