Labarai
Idan Buhari Da El-Rufa’i Sun Ba Ni Mota Su Tona Min Asiri – Sheikh Bala Lau
Shugaban Kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kalubalanci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai da su fito su bayyana cewa, sun ba wa Malaman kungiyar Motocin alfarma bayan kiran da suka yi na cewa ‘yan kungiyar su zabi Buhari.
A wani sako da kungiyar ta wallafa a shafinta, sun karyata wasu kafar yada labarai na yanar gizo marasa bin gaskiyar labari da suka yada cewa an ba wa Malaman kyautar Motocin alfarma.
Sheikh Bala Lau ya Kara da cewa, kowa ya yi da kyau ya sani.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com