Dalilin da yasa bana son auran mai kudi – Jamila Nagudu
Jamila babban dalilin da yasa bata son auran mai kudi shine saboda ba zai samu dama da lokacin tattali da tarairayarta ba
– Hazalika tace bata burin auran miji talaka, kawai dai ya kasance mai rufin asiri
Jarumar dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Jamila Umar Nagudu, ta bayar da dalilan da yasa bata son auran namiji mai kudi.
Jamila a wani shiri na Kannyflix ‘Mujallar Tauraruwa’ tace babban dalilin da yasa bata son auran mai kudi shine saboda ba zai samu dama da lokacin tattali da tarairayarta ba..
Kan irin mijin da take son aure tace “Bana son auran miji mai arziki, haka kuma bana son auran miji talaka”.
“Ina so na auri mutum da zai dauki nauyin bukatuna ciki harda samun lokain zama tare dani. Bana son miji mai tarin dukiya da yawa saboda yawan harkokinsa ba zai bari ya samu lokaci na ba, ” inji ta.
Jamila ta fito a fina finai da dama kamar irin su Miji Da Mata, Wani Gari da kuma Jamila Da Jamilu.