Labarai

An Fara Bincikar Tsohon Sifetan ‘Yan Sanda Kan N322m Ta Zabukan Bana Da Sukayi Batan Dabo

Mukaddashin sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu a ranar alhamis ya bukaci ‘yan kungiyar da tsohon sifeta janar Ibrahim Idris ya hada don zabe dasu yi bayani akan yadda suka raba Naira Miliyan 311.649 da aka ba kwamitin.

Majiyar mu ta hedkwatar jami’an tsaro tace an kira wasu ‘yan kwamitin sun kuma amsa tambayoyi sannan suka koma guraren aiyukan su. Majiyar tamu bata bayyana mana ‘yan kwamitin guda nawa suka amsa kiran ba da matsayin su.

Sabon Sifeta janar din ya ba DIG Mohammed Katsina umarnin yi musu tambayoyi.

Amma wata majiyar tamu mai karfi tace shugaban kwamitin wanda kwamishinan ‘yan sanda ne bai amsa kiran ba saboda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara yankin shi. Har yanzu dai bamu ji dalla dallar tambayoyin da akayi musu ba.

Binciken majiyar mu ya gano cewa tsohon sifeta janar na ‘yan sanda ya rubuta wasika game Shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Disamba 2018 da bukatar kudin.

Majiya mai karfi tace an bawa kwamitin kudin da suka bukata.

Tsohon IG Idris yasa wa kwamitin suna “Binciken barazanar kafin zabe da kuma dabarun tsaro na magance su”.

Kwamitin ya samu shugabancin kwamishinan ‘yan sanda da wasu kwamishinonin ‘yan sanda biyu tare da mataimakan kwamishinoni uku.

Rahoto : daga Hausadaily post

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button