ALHAMDULILLAH shugaban ‘kasar Nigeria Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban rundinar ‘yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu
Maigirma shugaban ‘kasarmu Nigeria Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban rundinar ‘yan sanda IGP Muhammad Abubakar Adamu bayan Maigirma IGP Ibrahim K. Idris Ya kammala wa’adin aikinsa
Hakika tarihi ba zai taba mantawa da kokarin da IGP Ibrahim K. Idris yayi ba, muna godiya sosai gareka Oga, ba komai kaje ka huta muna fatan Allah Ya biyaka da Aljannah
Sai dai ina yiwa manyan maciya amanar Nigeria masu daukar nauyin kwangilar manyan laifuka albishir da cewa dodon ku yazo, domin sai kun gwammace da ma IGP Ibrahim K. Idris ne ba wannan ba
Muna rokon Allah Ka taimaki sabon shugaban ‘yan sandan mu IGP Muhammad Abubakar Adamu
Allah Ka zama jagora a gareshi Ka bashi ikon tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin ‘kasarmu Nigeria Amin