Kannywood

Sharhin Fina Finai :Sharhin Fim Din ‘Atine’

Suna: Atine
Tsara Labari: Hamza Gambo Umar

Kamfani: Media Suite Art

Shiryawa: Hussaini Ibrahim

Umarni: Tijjani Mai Jama’a

farkon fim din an nuna Hajiya Bushira wato uwargidan Alhaji ta biyo Atine ‘yar aikinta da katako tana dukan ta saboda wani laifi da tayi mata, a daidai sannan ne Rakiya mahaifiyar Atine wadda itama take aikatau a gidan Alhaji ta nufo wajen su tana nuna wa Hajiya Bushira rashin dacewar dukan da take yiwa Atine da katako, amma sai Hajiya Bushira ta mare ta gami da nuna mata cewar itama bata wuce duka ba bare ‘yar ta Atine. Ganin hakan ne yasa Atine ta soma nuna wa mahaifiyar ta cewar subar gidan saboda ‘yan aiki basu da daraja a gidan, amma sai mahaifiyar ta Rakiya ta nuna rashin goyon bayan ta akan hakan.

Atine taje wajen dan uwan mahaifiyar ta Malam (Sulaiman Bosho) ta roki ya ajiye ta a gidan sa ko aure ne yayi mata, amma sai ya kireta ya nuna babu ruwan sa da damuwar ta. Yayin da Atine kuma da mahaifiyar ta suka cigaba da fuskantar matsala a gidan Alhaji domin ko zama a falo Hajiya bata yarda su yi ba matukar mijinta yana nan. Wata rana amaryar Alhaji (Hamza Indabawa) wato Sakina ta saka Atine aiki sai Hajiya tazo itama tana bukatar Atine tabar aikin da take yi taje yin nata, amma sai Sakina taki yarda da umarnin Hajiya, ganin hakan ne ya fusata Hajiya ta daga hannu zata mari Sakina amma sai Sakina ta rike hannun tare da gaya mata miyagun maganganu, hakan ne yasa Hajiya taci alwashin daukar mataki akan Sakina, sai dai kuma bayan Hajiya ta fadawa Alhaji abinda ke faruwa gami da karawa da wani sharrin sai Atine ta karyata ta gami da nuna cewar Hajiya ce taci mutuncin Sakina gami da dukan ta, jin hakan ne yasa Alhaji ya fusata ya mari Hajiya gami da ba ta rashin gaskiya, faruwar hakan kuma ta kara rura wutar kiyayya a tsakanin Hajiya da Atine, Hajiya tayi ta yunkurin ganin ta rama cin mutuncin da Atine ta jawo mata amma mijinta da kishiyar ta Sakina sun ki bata goyon baya akan hakan. Kwatsam wata rana a cikin dare rashin lafiya ta kama Rakiya mahaifiyar Atine, rashin samun  kulawar gaggawa daga wajen mutanen gidan ne yasa Rakiya ta mutu. Tun bayan rasuwar ta abubuwa suka kara dagulewa Atine, domin kullum cikin kyara da tsangwama take a wajen Hajiya wadda har rokon mijinta tayi akan ya kori su Atine amma yaki yarda da hakan.

Hajiya Bushira mace ce mai tsananin kishi wanda hakan yasa a duk lokacin da Alhaji yayi niyyar karin aure sai Hajiya tabi duddugi ta lalata abin. Ana cikin haka a wani dare Alhaji ya nufi dakin Hajiya Bushira amma taki bude masa kofa saboda wani laifi da yayi mata, yaje wajen amaryar sa Sakina ita kuma taki yarda ya shiga dakin ta saboda ba ranar girkin ta bane, faruwar hakan ne yasa Alhaji ya shiga dakin Atine yayi tarayya da ita wanda dalilin hakan ne yasa idanun Atine suka fara budewa ta daina jin tsoron kowa a cikin gidan, ya zamana cewa ko siyayya Alhaji zai yiwa su Hajiya sai Atine ta nuna zata raka sa, haka idan sun fita zasuyi ta hirar soyayya ita da Alhaji. Cikin lokaci kadan Atine ta soma yiwa su Hajiya rashin kunya, ko aiki suka sanya ta sai taga dama zatayi, haka ma takan fita unguwa a duk lokacin da ta so.

Ana tsaka da haka ne Atine ta samu juna biyu, kuma ta nuna wa su Hajiya cewar mijin su ne yayi mata ciki, amma bayan su Hajiya sun rutsa shi da tambaya sai ya amsa cewar juna biyun sa ne kuma yaci alwashin zai auri Atine. Jin kudurin sa ne yasa Hajiya Bushira da Sakina suka shiga dakin Atine tsakar dare suka danne mata kai da filo har sai da ta daina motsi, a sannan ne juna biyun jikin ta ya zube suka dauke ta a mota suka jefar da ita. Sai dai kuma bayan sun dawo a sa’in da Alhaji ke neman Atine su kuma suna ganin cewar sun kashe ta. Kwatsam sai ga Atine ta dawo gidan tare da abokin Alhaji. Ganin bata mutu bane yasa tsoron Allah ya shiga zuciyar su Hajiya suka saduda kuma suka roki gafarar Alhaji da Atine gami da mika wuya akan auren Atine wanda mijin su ya shirya zai yi. 

 Abubuwan Birgewa:

1- Fim din ya nishadantar kuma ya fadakar. Labarin ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isar wa, kuma an yi kokarin rike me kallo ta yadda zai so ganin abinda zai faru a gaba.

2- Kalaman jaruman sun yi dadi wato (Dialogue)

 3- An samar da wuraren da suka dace da labarin.

4- Camera ta fita radau.

 5- An nuna illar daukar ‘yan aiki, musamman ‘yan aiki mata a cikin gida.

  Kurakurai:

1- An samu matsalar daukewar sauti a wasu wuraren daga cikin sina sinan (scenes) fim din.

2- Lokacin da su Hajiya suka jefar da Atine bayan sun danne kan ta da fillo da zaton ta mutu, me kallo yaga Atine sun dawo gidan tare da abokin Alhaji wanda shine ya tsinto ta, ya kamata ace wani mutum ne can na daban ya tsinto ta ya rako ta gida ba abokin Alhaji ba, domin ba lallai ne ace wajen da su Hajiya suka jefar da Atine har a iya samun wani wanda ya santa a wajen ba.

3- Yarinyar da ta fito a matsayin Atine fuskar ta ba ta iya bayyana damuwa ko wani alamu na tausayi wato (Emotion), ya kamata ace yanayin halin matsin rayuwa da takan shiga a wasu lokutan hakan ya bayyana akan fuskar ta ko don me kallo yaji a ransa kamar a zahiri ne abin ke faruwa da yarinyar ba wai a fim ba.

 4- Shin Alhaji bai taba haihuwa bane? Me kallo yaji Hajiya Bushira ta taba gayawa amaryar ta Sakina cewa ko dan ta dake karatu a kasar waje ya girmi Sakina din, sai dai kuma har fim din ya kare ko sau daya ba’a ji Alhaji ya ambaci cewar yana da da ba, haka kuma ba’a ga dan ko sau daya yazo hutu gida ba, sannan kuma lokacin da Atine tayi cikin shege me kallo yaji tana yiwa su Hajiya gorin haihuwa tana cewa sai dai su ci abinci su yi kashi. Ya kamata a fahimtar da me kallo gaskiyar lamari ko don a fitar dashi daga wasu wasi. 

Karkarewa:

Fim din ya fadakar kuma ya nishadantar,   labarin ya tafi kai tsaye har ya dire bai karye ba. Sannan kuma an yi kokarin nuna wani darasi na wata matsala wadda ta shafi al’umma.   

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button