Uncategorized

Samfuran Kalaman Soyayya

Samfuran Kalaman Soyayya
Samfuran Kalaman Soyayya

 Amincin Allah da kariyarsa da yaddarsa su tabbata ga sarauniyar kyawawa. Tauraruwa mai haskaka duniya. Gani nazo gareki ko na samu jin daddadan kalamanki masu sanya nutsuwa ga mai sauraro. Sannan naga kyakkyawar surar da Allah ya baki wadda ke samar da farin ciki da nishadi ga mai kallo. Taku kike tamkar sarauniya, ina so nayi amfani da wannan damar na bayyana miki yadda sonki yake a cikin zuciyata, sonki yabi jijiya ya ratsa tsoka ya fasa kashi da bargo da ke nake rayuwa sonki shi ne ya zamto jinin jikina. Yabonki shi ne abincina begenki shi ne ruwan shana, kaunarki ita ta zamto min numfashi na, my one ba zan iya rayuwabaa idan babu ke kece farin ciki na da tunaninki nake kwana da yabonki nake tashi da zancenki nake yini duk motsina naki ne kece farin cikin zuciya ke ce abar alfaharina kece kadai idaniyana ke iya gani, ki tallafawa dan marayan da ya rasa duk wani farin ciku don ganin ya sameki. Kece kadai zaki iya dawomin da farin ciki na da walwalata da dariyata idan kikace bakya sona zan rasa rayuwata.

 

Zuwa ga bakuwar zuciya mai kyakkyawar fuska hadi da kyakkyawan suna mai dadin kamshi mai kyakkyawan Murmushi mai zazzakar murya, ita ke sani na manta komai. Haka kyawawan idanuwanki sukansa na zamanto makaho a yayin da suka yo arba da kyakkyawar mace tana kusanto almajirinta, idan naji an kira sunanki sai naji wani nishadi tamkar an yimun albishir da aurenki, duniyar masoya kizo muyi shigewa ki sani a hannun dama domin jini da jijiya hadi da duk kaina farin ciki na idan na tunaki sai naji wani shauki ko aiki ki yarda da ni ki sani a cikin zuciyarki sarauniyar mata. 

Sallama da fatan budewar kofofi tare da farin ciki a gareki tare da farin cikin mai girma gami da annashuwaa gareki diyar girma a wajena, Boyayyen sirri ne zan bayyana a gareki saboda nazarin da nayi akanki my dear, duk-kan bishiyoyi da tsuntsaye da ruwan sama Allah ya halicce su ne dan mu mutane mu rayu haka kuma numfashi da lafiya ba’a sayensu saboda sun zama dole ga rayuwa haka ita soyayyar gaskiya ba’a siyanta da kudi baiwa ce daga Allah yanzu idan nace kin dauke kaso mafi tsoka wajen sanyaya farin cikina ya zaki ji? Tun lokacin dana fara cin karo da ke kwarjininki yake ta bugun zuciyata, da yawa saina ji murmushi ya cikan fuskata idan na tunoki, me yasa hakan? Ni dai nasan a kowanne lokaci ina yaban halayenki musamman sanin girman mutane da kulawa, amma idan nace sunanku shine mafi yayi da yawan ambato a cikin birnin zuciyata ya zaki ji? Ki sanar da ni maganin damuwata ma’ana ki mallakamin zuciyarki hakan kadai zai kawo waraka a gareni. Ko sunanki kadai ya isa ya isar da sakon so nakan ji nishadi mara misaltuwa yayin jin sunanki bare kuma kallonki daban kike da sauran mata a duk lokutan da naji an kira sunanki a kusa da ni nakanyi kyautar da duk abinda ke hannuna a lokacin koda kuwa gidan mu ne, amma abu daya ne ba zan iya bayar da shi ba ga kowa saboda mallakin kine ke daya yake annurin idanuwana dama gangar jikina gaba daya ba komai ne ba face zuciya ta, da na rasaki a matsayin masoyiyata gwara na rasa kudin sayen komai nawa zuciyata ta dade tana tanadi ga mace mai suna irin naki zanso ki aminta ya soyayya ta kiga irin tanadin da zuciya ta tai miki ya masoyiyata zan tarai-rayeki kamar yadda masoyan india ke tarairayar ‘yan matansu a film idan har kika amincewa soyayyata. Ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har sai lokacin dana rufe idona wanda ba zan kara bude su ba har abada ballantana nayi tozali da kyakkyawar surar jikinki da tattausan murmushinki wanda da mutum yana halitta da za’a iya cewa ke kika tsarawa kanki komai ba tare da tawaya ba. Hausawa sunce dan Adam tara yake bai cika goma ba, to ke a wurina kin kai 100% hakika yin maganarki da godiyarki a gareni yafi bani duk wani abu da yake cikin duniya. Nasan a cikin masu neman zuciyarki nine makaskanci a wurin rubutu sannan nakasasshe a wurin kalamai, hmm! Ina ma ana iya rubuto zuciya a turo da ita da ananne za ki iya tantance masoyi na gaskiya sauran duk gwadawa suke amma ni aikatawa nake. 

A dukkan fadin duniya ba a yi suna mai dadin naki ba, ba’a taba mace mai kyawunki ba wanda aka rasa kalmomin da za a yi amfani da su wajen bayyana irin kyawun da Allah ya yi miki ba, idan aka tsaya za a auna irin kyawun da Allah ya yi miki za a gane cewa masu iya magana sun yi karya da suke cewa “kyawun yana disashe wa” da ba su cire kyau naki ba, domin wanda yake auna lokacin disashewarsa a haka lokacin sa zai kare na rayuwa ba tare da ya gano komai a kan kyawun ki ba, saboda kina da ilimi da zaki iya tafiya da akalar rayuwata ta yadda kyawunki ba zai disashe ba, saboda kyawun yana dishewa ne lokacin da aka tsufa ba tare da bin dokar Allah ba, ke kuma rayuwarki kur’ani ce da hadith Manzon (S.A.W) kawai abu daya kike da bukata shi ne ki sami masoyi da zai dauke ki daga wannan duniyar ta yaudara da cin amanar soyayya izuwa sabuwar duniyar nan mai dauke da ababen more rayuwa irin su labbuna masu korayen ciyayi da koramu da ‘ya’yan itatuwa da kuma kukan tsintsaye wanda zai sa ka manta an halicci wani abu wai shi bakin ciki, ba wanda kuma zai iya kaiki wannan duniya sai ni, saboda haka naga na dace da zama sarki a cikin masarautar zuciyarki da fatan iliminki zai zama akalar zaben wanda ya dace da sarautar zuciyarki. Fatan alkhairi ga macen data cancanta a kirata da sarauniyar kyawawan ‘yan matan africa ta dalilin martabar da surarta ta samu sakamakon kasancewarta mace me santalelen goshi me haske wanda ya dace da madaidaiciyar fuskarta kuma gashi mayalwatacce yake binnkasan keyarta me albarka, idanuwanta suke lumshe akan kasan fatar da ke jikin lallausan kumatunta mai haske da tsananin sheki ga madaidaicin baki mai albarka wanda ya zamto abin yabo ga zuciya ta ko da kuwa ba na tare da ita. Ga kuma kyawawan halaye da suka kasance tamkar suffar tata. 
wadannnan dalilan su suka sa tunani na ya kamu da ciwon tunani, ya kamu da tsananin takura da rashin suku ni, dan baki na ya gaza fitar da boyayyen sakon da ke kasan zuciyata a gare ki tsabar matsanancin kwarjinin da ya tare a gare ki ya ma’abociyar nutsuwa da kamala. Da fatan dan guntun bayani na zai sa ki amince ki ba ni dama na bayyana karamin sakona a gare ki ya macen da babu mai kyau tamkar ta duk fadin duniya. Kadan daga kalaman soyayya ku kasance tare da ni a mako mai zuwa cikin wannan shafi naku na Soyayya da Shakuwa.  

 TAMBAYAR YAU TANA CEWA 

Kawo naka kalaman masu karawa masoya shaukin soyayya, kema kawo naki kalaman dan karfafawa masoya soyayyarsu. Tsakanin Mata da maza waya fi iya kalaman soyayya? Sai na ji daga gare ku.   

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button