Rashida Maisa’a Ta Zama Gwarzuwar Gasar ‘ZAFAA Awards 2018’
Fitacciyar jarumar finafinan Hausa kuma jigo a cikin jam’iyar APC a jihar Kano, Hajiya Rashida Adamu wadda ake yiwa lakabi da (Mai sa’a) ta samu nasarar zama gwarzuwar gasar finafinai ta zafaa award 2018 wadda aka gudanar da ita a birnin London na kasar Burtaniya. A kashen watan nuwamban da ya gabata ne dai aka shirya taron na fitar da gwaraza na gasar zafaa global award wadda gasa ce ta duniya da ake karrama ‘yan fim da masu harkar nishadantarwa da ma wadanda suke bada wata gudunmawa da ta shafi al’umma kai tsaye a duk fadin duniya. Hajiya Rashida mai sa’a tana daya daga cikin ‘yan fim a masana’antar finafinai ta Kannywood da suka samu lambar yabo a wannan gasa da aka yi ta bana in da ta samu kambu karramawa a sakamakon bada gudummawa da take yi ga mabukata a karkashin kungiyarta ta gidauniyar mai sa’a.
Bayan dawowarta daga birnin landon inda ta je domin karbo kambun karramawar wakilin mu ya nemi jin ta bakin ta a game da tafiyar ta da kuma abbuawan da ta kunsa inda ta yi mana bayanin cewar: “To kamar yadda aka gani a hotuna da suke yawo a soshiyar media wata gayyata ce na samu daga kungiyar zafaa global award 2018 da take karrama ‘yan fim a duniya kuma ina godiya ga Allah da na samu gayyata daga wajensa akan irin abubuwan da nake gudanarwa a bangaren gwamnatin jihar Kano, da kuma ayyukana na gidauniyar mai sa’a don haka suka kirawo ni suka karramani saboda namijin kokarin da nake yi akan masu karamin karfi don haka sai suka tura min katin gayyata na ji na yi biza kuma gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyina na je aka gudanar da taron, kuma mun samu ganawa da manyan mutane har ma da jakadan Najeriya da yake zaune a kasar mun samu ganawa da shi har ya gayyace ni gidansa ya shirya min wata walima don haka ina godiya da wannan karramawar da aka yi min. Ina fatan kuma na rinka samun sa’ar da zai zama duk shekara sai naje na karbi wannan award din, kuma ina godiya ga Gwamnatin Kano a game da daukar nayina da ta yi wajen wannan tafiyar hakan ya nuna goyon bayan da ake bani kuma an san abinda nake yi. Shi yasa aka samar mini da hanyar da zan tafi a lokacin dana samu katin gayyata, don ka ga a lokacin da aka turo min da katin gayyata ya rage sauran kwana shida a yi taron kuma bani da biza, amma dai cikin gaggawa aka yi min har na samu tafiya don haka ina alfahari da wannan. Ta cigaba da cewa, “Hakan ya bani wani kwarin gwiwar da yardar Allah sai na zagaye duniya ina karbar award domin abubuwan da nake yi ina yin su ne da gaske kuma Allah yana duba zuciyar masu kyakkyawar niyya. Daga karshe ta yi godiya ga duk mutanen da suka bada gudunmawa a wajen tafiyar tata musamman gwamnatin jihar Kano da kuma Hajiya Hadiza wadda tana daya daga cikin masu bibiyar ayyukan da mutane suke yi domin a karrama su don haka ta yi godiya a gare ta da ta buga aikinta kuma ta ga ta cancanta da a karammata sannan sai ofishin Nigeria na kasar Burtaniya da sauran kungiyoyi da suke hade da su a can wadanda suke bata gudunmawa ba kadan ba don kuwa a cewar ta tun da ta je har ta dawo mutane ne suka dauki nauyin ta ko ruwa ba ta saya da kudinta, ba abin haka na mika godiya a gare su haka na ‘yan media da suka rinka dora hotunanta na ‘award’ da ’yan fim irinsu Kamal S. Alkali, Nazifi Asnanic, Ali Nuhu, Maryam Yahaya, Aisha Tsamiya, Rukayya Dawayya, Maryam Jankunne, Saima Muhammad, Zahara’u Shata, Ummi Nuhu da ’yan fim irin su Kuliya Nura Gaya, Danfillo da dai sauransu, Ina godiya ga kowa. Allah ya bar zumunci.