Kannywood

Rahama sadau Tayi Murna Samun Mabiya Miliyan Daya A instagram

Fitacciyar ‘Yar wasan fina-finan Kannywood da Nollywood Rahama Sadau ta jinjina wa masoyanta da sauran masu bin ta a shafinta ta Instagram bisa murnar samun mabiya miliya daya a wannan mako.

Rahama ce mace ta farko a farfajiyyar fina-finan Hausa da ta kai yawan mabiya har miliyan daya.

Hadiza Gabon ce ta ke bi mata da yawan mabiya sama da 800,000 sai kuma jaruma Nafeesat Abdullahi da take da yawan mabiya har 700,000.

Tuni dai Rahama ta yi fice a harkar fina-finai duk da cewa ta shigo harkar ne daga baya-baya amma a halin yanzu babu jaruma kamarta da ta ratsa cikin jaruman kudancin Najeriya har da kasashen waje kuma ta yi fice a wannan sana’a.

A yanzu Rahama ta fada tsundum cikin harkar kasuwanci inda ta kaddamar da kayan shafe-shafe da kwalliya na mata.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button