Uncategorized

Nasiha: Kafin Ki Nemi Saki Daga Maigida, Ki Yi Tunanin Wannan…

 Shi dai aure a halin yanzu ga Hausawa/Fulani duk da cewa bisa turbar addinin Musulunci ake dora da gudanar da shi, amma kusan kashi 7 ciki 10 al’adu ke masa wurin zama, kama tun daga neman auren, zuwa bayarwa da shirye-shiryen auren da sauran hidindimu da kuma rayuwar zaman auren ta fuskar tanadar wurin zama da ilmantarwa da zamantakewa baki daya. Ba kuma wani abu ya sa al’adu suka yi katutu a cikin rayuwar aure da saki ba sai saboda duhun jahilci da lalaci da ya mamaye al’ummar tamu. Jahilci ne mace ta nemi saki da kanta a gurin majinta. Kafin ki nemi saki to ki nemo amsar wadannan tambayoyin kamar haka:

 – Shin idan mun rabu wa zan aura? – Wanda zan aura shin zai yadda na je masa da yara gidansa?

– Idan ya yarda shin mahaifin yaran zai yarda na je masa da yaran wani gidansa? – Idan ya yarda wa zai dauki dawainiyar su ta yau da kullum?

 – Su yaran za su dauki sabon mijina a matsayin uba?

 – Idan na maida su gidansu wa za ta rike min su?

 – Shin idan mun rabu haka zan dawwama ban yi aure ba don kawai na kula da yarana? Yan uwa mata ya kamata mu ce a’a ga zawarci. Gidan miji sak zawarci sam!.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button