Likafa ta cigaba Masarautar Kano Za Ta Yi Wa Nazir M Ahmad Nadin Sarauta
A kasar Hausa mawaki yana da matsayi babba kamar yadda yake da matsayi a sauran al’umma.
A Bahaushen tunani, Masana suna kallon kida da waka tamkar jini da tsoka ce a rayuwar Hausawa. Wato waka a zaman gargajiya ta zama tamkar shika-shikan matakan tsarin zamantakewa, wanda har ake zaton da rabi jini, rabi barci ne, to za ka taradda Bahaushe na rera waka a cikin barcinsa. Saboda tasirin waka ne ma ga zukatan al’umma, har ya zama kusan kowane rukuni da matsayin na ajin zamantakewa na ruwar al’umma ya na da nau’in Mawakansa.
Mawaki yana zama garkuwa ga jama’arsa da kare mutuncin jama’ar ko zuga su, su tashi su yi aiki nagari, kamar yadda mawaki yake kokarin kare wani shugaba idan wannan shugaban mai adalci ne ga jama’arsa.
Fitaccen Mawaki Naziru M.Ahmad, Wasu Masana da manzarta wakokin gargajiya sun bayyana shi a matsayin mawakin da ya fi kowane matashin mawaki bada gudummuwa a bangaren wakokin sarakuna, wanda a wannan karnin da muke ciki indai za a bayyana mawakan Sarakuna ko shakka babu Naziru M. Ahmad zai zo na farko. Mawakin ya yi wakoki bila adadin a wasu daga cikin masarautun kasar nan da na wajen kasar.
Idan masu bibiyar wakokin mawakin ba su manta ba, mawakin shi ne wanda ya taba yin wani baiti a wakar sa ta ‘Dan Majen Kano’ kuma maganar ta tabbata cikin ikon Allah, inda ya ke cewa: “A Sannu dai wataran Dan sarki, sarki ne” a wakar da yi yi wa mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi lokacin yana Dan maje kafin ya zama sarkin Kano.
Bayan su Mawakin ya yi wa sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi wakar nadin shi wato wakoki irin su: Baharahube Sabon Sarki” “Mata ku dau Turame” da sauran su. Wanda a lokacin da ya yi wakokin kowa ya san irin yadda wakar ta karade ko ina kuma ta yi yawo kamar wutar bazara.
Saboda biyayya da soyyaya da mawakin ya nunawa Sarki tun yana Dan Maje har ya zama Sarkin Kano, hakan yasa Masarautar za ta nada Mawakin Sarautar “SARKIN WAKAR SARKIN KANO” Za a yi nadin nadin ne a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba 2018 a fadar mai martaba Sarkin Kano. Allah ya nuna mana lokacin, amin.
Sanarwa daga kwamitin tsare-tsare; @yaseenauwal
@falalu_a_dorayi