LA’ANTAR Sheikh Gummi : Mahaifin Nura Hussaini Ya Nemi Gafarar Dr Ahmad Gumi
Mahaifin Dan wasan Hausa Fim Nura Hussaini wato Malam Hussaini Kano, ya taso takanas tun daga Birnin Kano zuwa Kaduna, domin nesanta kanshi daga tanbelen da Dan shi Nura yayi ta hanyar aibanta sanannen Malamin addinin Musulunci Dr Gumi. Dattijo Malam Hussaini ya ziyarci Babban Masallachin Juma’a na Sultan Bello dake garin Kaduna inda Dr Ahmad Gumi ke gabatar da karatu, sannan cikin hawaye ya nemi yafiya da afuwa na abinda Dan nashi yayi, na kasa samun bacci da natsuwa a rayuwata tun bayan ganin yadda ake yawo da Hotunan Nura yana zagin Babban Malami, na yiwa Dana fada kuma yayi nadamar abinda yayi, wannan ne ya sanya na taso musanman zuwa wajen Malam domin neman gafarar abinda Dana yayi, Don Allah Malam ka yiwa Dana afuwa. Da yake maida jawabi, Dr Ahmad Gumi ya tabbatar da yin yafiya da afuwa ga Nura Hussaini, sannan ya bukaci sauran Jama’a musanman daliban shi da su janye duk wata adawa da Nura sakamakon neman afuwa da mahaifin shi yayi, sannan daga karshe yayi addu’a ta neman shiriya da albarka ga Nura Hussaini. Ga bidiyon