Labarai

Jirgen Yakin Nigeria Suna Ruwan Wuta A Yakin Baga Na Jihar Borno

Yadda kafofin watsa labarai har da su BBC suka fitar da labarin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram bangaren ISIS reshen ISWAP sun karbi ikon garin Baga har ma sun kafa tutarsu a garin sannan suka jagoranci sallar asuba to ya kamata su fito su sanar da duniya halin da ake ciki yanzu

Domin halin da ake ciki yanzu a Baga shine bayan dakarun sojinmu sun janye saboda dabarun yaki, rundinar sojin saman Nigeria ta fara kaddamar da mummunan hari da manyan jiragen yakin Nigeria irinsu “Alpha Jet” da “Mi 25 Attack Helicopters” akan ‘yan ta’addan da suke Baga suka kafa tuta

Akwai sansanin sojoji da dama a Baga har da sansanin sojojin ruwa, kuma nan ne cibigar rundinar hadin gwiwa (MNJTF) na kasashen dake iyaka da yankin tabkin chadi yake, janyewar da sojojin sukayi kofar rago ne ga ‘yan ta’addan, yana da alaka da dabarun yaki na sojoji

Tun a jiya jiragen yakin Nigeria suka fara kaddamar da hari a garin Baga, kuma an gano wasu gungun ‘yan ta’adda sun nufi Doron-Baga jirgin yaki ya bisu ya harba musu manyan makamai masu linzami kuma an samu nasaran tarwatsasu

Kuma an kara yawan sojoji a inda dakarun sojinmu suka ja daga a yankin na Baga, sannan sojojin saman Nigeria da suke sarrafa jiragen yaki a sararin samaniyar yankin Baga suna musayar bayanai tsakaninsu da sojojin ‘kasa, da zaran sojojin saman sun gama kaddamar da hari sojojin ‘kasa ‘yan kundunbala zasu kutsa cikin garin na Baga tare da manyan makaman atilari su kawar da duk wani burbushi na ‘yan ta’addan

Wannan shine yanayin da ake ciki a Baga, kuma sojojin Nigeria su ke da nasara, ba kamar yadda kafofin watsa labarai wadanda suke taya ‘yan ta’adda yada farfaganda suka yada ba

Allah Ka taimaki dakarun sojojinmu Ka basu sa’a da nasara akan ‘yan ta’adda da wadanda suke taya ‘yan ta’adda yada farfaganda.

Daga: Datti assalafiy

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button