Gaskiyar Lamari Game Da Hotunan Maryam Booth Da Sadiq Zazzabi
Jaruman a cikin sabbin hotunan da suka yi tare sun jawo hankalin jama’a inda da yawa ana hasashe cewa akwai wani alakar soyayya dake tsakanin su.
Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth da shahararren mawaki Sadiq Zazzabi sun mamaye kafafen sada zumunta bisa ga dalilin hotunan da suka dauka.
Jaruman a cikin sabbin hotunan da suka yi tare sun jawo hankalin jama’a inda da yawa ana hasashe cewa akwai wani alakar soyayya dake tsakanin su kuma hotunan na kafin auren su ne.
Masoyan jaruman da masu bibiyan labarun dandalin fina-finan hausa suna ta masu fatan alheri da zaton cewa suna shirin bikin auren su.
Sai dai alamu sun nuna cewa hasashen da jama’a keyi game da hotunan ba gaskiya bane.
Shafin Kannywoodexclusive ta bayyana cewa jaruman sun dauki hotunan ne domin shirya ma wata sabuwar shiri da shahararren mai gabatar da biki Mc Ibrahim Sharukhan ke shiryawa mai taken “gidan biki”.
Shima Mc Ibrahim ya gasgata hakan inda ya wallafa hotunan jaruman a shafin sa na instagram tare da rubuta “Allah ya kaimu gidan biki”.
Kamar yadda masu karatu zasu gani, hotunan dai sun birge kuma shahararren mai hoto Umar Balancy ya dauki hotunan wanda da hakan jama’a ke ganin cewa lamarin gaskiya ne.