Labarai

An Gudanar da Bukin Bayyana sakamakon Kidayar Buhun Gero a Garin Yauri dake Jihar Kebbi a Yau

Yanzu haka an Kambala  bukin bayyana sakamakon Kidayar Buhun Gero a Garin Yauri dake Jihar Kebbi, wanda wasu matasan Garin Yauri, sunkayi Kirga kuma Yau sun bayyana sakamakon ko Kwara nawa ke cikin Buhun Gero.

Babban Bako Mai Jawabi Shine Prof. Aliyu Muhammad Bunza kuma yayi Jawabi Mai Gamsarwa da kuma jinjinama wadannan Matasa.

Sannan Maimartaba Sarkin Yauri Dr. Zayyanu Abdullahi shima yayi Jawabi a wurin Bukin inda shima yayi yabo da Jinjina ga Matasa, ina ya kara dacewa wannan aiki na Kidayar Buhun Gero tamkar Magani Zaman Banza ne harda in ankayi La’akari da duk matasanda sunkayi wannan aiki sunada Sana’ar yi.

Kuma Bukin yasamu Wakilcin Maigirma Gwamnan Jihar Kebbi Sen. Atiku Bagudu wanda Kwamishinan Yada Labaru na Jihar Kebbi Hon. Gado Marafa ya Wakilta. Inda Wakilin Gwamnan Jihar Kebbi ya Bayyana dacewa Gwamnatin Jihar Kebbi shirye take ta taimakama Matasan Jihar Kebbi da duk wani aikin Alheri da sunka kirkiro Don daga martabar Jihar Kebbi da kuma kasarmu Najeriya a idon Duniya.

Miliyan goma sha daya, da Dari tara da saba’in da tara, da dari takwas da sittin da takwas(11,979,868) ke kicin Buhun Gero.

                      
Miliyan Biyu, da Dari uku da tis’in da Biyar, da Dari da saba’in da uku, da kwara shida (2,395,973,6 ) kowane Damen  Gero.

Matasan su 37 ne, sunyi kwana 107  wajen Kidayar Buhun Geron.

Daga Karshe Shahararren Mawakin Masarautar Yauri Alh. Ibrahim Sani Dandawo shima yayi Waka akan Bukin Kidayar Buhun Gero a Garin Yauri.

Shatane Auwal Yauri ya taimakamin wurin hada wannan Labari da kuma Daukar Hoto.

Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button