Kannywood
Shin Da Gaske Ne Akon Da Rahama Sadau Suna Soyayya?
Advertisment
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa da na turanci Rahama Sadau ta musanta batun da jama’a suke na cewar akwai alaka ta soyayya tsakaninta da fasihin mawakin nan dan kasar Senegal wato Aliane Damala Bouga wanda aka fi sani da Akon.
Jarumar tayi wannan batun ne dai a hirarta da Aminu Sharif na sananniyar tashar Talabijin din nan wato Arewa24 a cikin shirin su na kundin kannywood na ranar talata.Jarumar ta bayyana cewa bata taba tunanin haduwa da fasihin mawakin ba, duk da dai dama ta san shi saboda sauraron wakokin shi da take yi.
“Ban taba tunanin zan hadu da Akon ido da ido ba. Na sanshi tuntuni saboda dama ina sauraron wakokin shi sosai. A lokacin da naga katin gayyata daga Akon nayi farin ciki sosai, saboda banma yadda ba da farko, nayi matukar mamaki sosai.”
Da aka tambaye ta ko meye gaskiyar cewa Akon din yayi yungurin mayar da ita addinin Kiristanci, sai ta kada baki tace: “Duk masu fadar wannan maganar basu son Akon bane, domin ko Akon Musulmi ne mai kula da addini sosai”.
“Na samu labarin cewa a lokacin azumi yakan kebe kan shi don gudanar da ibada sosai yanda ya kamata. Kuma, a lokacin da na kai masa ziyara har gayyata ta yayi zuwa aikin umra amma ban karbi hakan ba saboda surutun mutane.”
Sources:arewamobile.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com