Lokacin Daya Fi Dacewa Masoya Suyi Sumbata (KISS)
Wato mafi yawan bincike abun da yake nunawa shine babu takamammen lokacin da yafi cancanta wajen sumbatar masoyi ko masoyi. Amma mafi yawancin masana a harkar soyayya sun bayyana cewa mako 1 da fara soyayya yafi cancanta masoya su sumbace junarsu amma kuma hakan ya iya kasance da irin yadda masoyar ke son junarsu a wannan lokaci.
Sumbace na farko abu ne mai matukar muhimmanci a harkar soyayyar don yana daya daga cikin abubuwan da ke kara dankon soyayya a tsakanin masoya. Idan an yi shi a lokacin da ya kamata, ya kansa masoya su ji dadin soyayya.
Idan an yi shi da wuri ba tare da jirin lokacin da ya cancanta ba ya kan kawo kiyayya a tsakanin masoya sannan kuma idan an dan jinkirta ya kan kawo tangarda a soyayyar domin sai a bar mutum a matsayin aboki kawai bayan niyyarsa daban a zuci.
Mace ta kan ba namiji alamomin daban daban idan ta shirya sumbatar namiji. Ta kan nunawa namjiji cewa a shirye ta ke wajen hada labba da masoyinta shi ya sa ya ke da kyau mutum ya gwada amfani da dokar da masana suke kira da suna 90/10 rule of kissing wato dokar sumbata 90 bisa 10.
Ita wannan dokar ana yinsa ne kamar haka: Namiji zai kai fuskarsa daidai kusa da fuskar masoyiyarsa hakan ne ake kira 90, idan har ta shirya sumbatarsa budurwar nasa za ta cikata saura 10 ta hanyar matsar da fuskanta kusa da na shi domin lebensu su hadu da juna.
Masana sun tabbatar da cewa masoya ko ma’auratan da suka baiwa Sumbata muhimmaci basu cika samun matsala ba hasalima Sumbata tana hana samar da kishi ta wata fuskar.
To amma Addinin Musulunci ya haramta kebewa da Macen da baka Aura ba bare har ta kai ga sumbata, sai dai ya halasta bayan Aure hasalima sunnace ku fara wasannin soyayya da matar ka kafin kwanciya.
Jaridar Dimokuradiyya 27-11-2018.