Kar Ku Auri MA’TA Kala [7]: Daga Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
1- AL-ANNA’NATU: Itace mace mai yawan qaryar ciwon kai, ko kuma ciwon wani abin daban, Alhali kuma qarya take yi, Babu Abinda ke damunta,
To tun kafin ka Aureta Idan ka gane ta da wannan halayen na qaryar ciwo don cimma wata manufarta to kayi hattara.
2-AL-MANNA NATU: Mace mai yawan gori ga mijinta, musamman idan tayi masa kyauta, ko tayi wani aikin dashi ya sata, wanda za kaga tana yawan cewa
“Na yi maka kaza da kaza ai.” Haka ma ranar nan nayi maka kaza ai”
To idan ka gane ta da haka to kayi mata Nasiha, Idan taqi dainawa to kayi hattara.
3-AL-HANNA NATU: mace mai yabon ‘ya’yan tsohon mijinta a gaban sabon mijinta, wanda za kaji tana cewa “ai yaran tsohon mijinta sun fi naka yaran” da dai sauran cin fuska, to ka hakura da ita yafi alheri.
4- QAI-ATUL QAFA: Macen da take da “Bad record” wanda ya kai ga duk jama’a suna ganinta da mummunan hali, da rashin qima, to kayi hattara da auren irin wannan matai.
5- AL-HADDA QATU: Macen da idan taga wani abu wanda take so sai ta tilasta ta takurawa mijinta yasai mata kota halin qaqa itadai yasai mata. Yawanci ana gane su saboda sune tin kafinka Auro su zaka ga tana damunka da sai ka sai mata kaza, ko sai ka bata kudin anko da dai sauransu,to kayi hattara da auren irin su.
6-AL-SHADDA QATU: Macen da take da yawan surutu, wadda bata riqe sirrin mijinta, Ana gane irinsu idan suna y’an Mata,
domin sune da zaran kayi sirri dasu za suje suna fadawa qawayensu.
7-AL-BARRA QATU: Mace mai yawan bata lokacinta a rayuwa wajen yin kwalliya,wanda zata dauki tsawon awanni tana shafe-shafe kamar zata canza halittar ta.
Kayi hattara da Auren irin wadannan!!! Inji “Sheikh Uthaymeen”.
“A Duba littafinnan mai suna “A Concise Manual Of Marriage”. By “Shaikh Muhammad Ibn Uthaymeen”.
Bawai Aurensu Haramun bane, Shaikh Uthaymeen Yana baka shawara ne akansu, daka auri irinsu
Gamma ka hakura yafi maka Alheri.
Allah Ya Sa Mu Dace Allahumma Amin.