Kannywood

Bana Gaba Da Fati Nijar – Inji Maryam Baba

Baya ga kasancewarta shahararriyar mawakiyar Hausa ta zamani, Maryam A. Baba tana taka muhimmiyar rawa wajen fadakarwa da nishadantarwa a fagen sana’arta. Kamar yadda ba a raba duniyar mawaka da ’yan fim da abin kwarmato, a ’yan kwanakin nan ne aka rika baza jita-jitar cewa mawakiyar ba ta ga maciji da abokiyar sana’arta, Fati Nijar.
Sai dai a wannan tattaunawa da Maryam ta yi da Aminiya, ta karyata batun, inda ta ce babu wata rashin jituwa a tsakaninsu. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:
Za mu so ki gabatar da kanki
Sunana Maryam A. Baba, wasu kuma kan kira ni da lakanin Maryam Sangandali. An haife ni a Unguwar Sani Mainagge, Kano. A nan na fara karatun Islamiyya ta Rabi’u Sipikin. Bayan sauyin wurin zama na yi makarantar firamare ta Babban Giji. Daga nan na tafi makarantar Arabiyya ta GGASS danzabuwa.

Daga nan na sami sauyin makaranta, na koma GGSS KABO, inda a nan ne na kammala karatuna na gaba da firamare. Daga nan na fara karatun Shari’ar Musulunci a makarantar Legal ta Aminu Kano. Daga bisani na ga karatun ya yi min tsauri sai na sauya sheka zuwa Kwalejin Sa’adatu Rimi ta Kano, a nan na yi karatun NCE. Daga nan na fara aikin wucin gadi da gidan talabijin na NTA Kano, na yi irin wannan aikin da gidan rediyon Freedom, sannan da Dala FM, duk a Kano. Yanzu kuma ga ni ina sana’ar waka.

Ko ya kika sami kanki a sana’ar waka?

Na fara waka tun a lokacin da muke makarantar Islamiyya, baya ga nan ina yawan sauraron wakokin Indiya; ina bibiyarsu da kuma lokaci ya yi aka fara amfani da waka a fina-finan Hausa sai na yi amfani da wannan damar ni ma na ce bari na shiga a yi da ni; domin na ba da gudunmawata ta hanyar waka.

Domin ita waka hanya ce ta isar da sako da akan yi gargadi, tunasarwa da tsoratarwa, baya ga nishadantarwa.
Saboda dimbin jama’a da suke saurare, tarin fadakarwar da ake samu a waka kan sanya wanda ke yin abin da ya saba ka’ida ya gyara; wanda yake yin abin da ya dace kuma ya kara kaimi.

Ko akwai alaka tsakaninki da Murja Baba?

Eh, alakarmu da Murja Baba ita ce sana’armu ta waka sai kuma addinin Musulunci da ya hada mu, wannan ita ce babbar alakarmu.

Ana maganar cewa soyayya ta kullu tsakaninki da Aminudeen Alan Waka, ko ya abin yake?

Ahhh, inji waye? Ehhh, Alan waka dai kamar dan uwa ne a gare ni kuma yana taimaka mini sossai a sana’ata ta waka. A taikaice dai yayana ne, wannan shi ne abin da yake a kasa.

Wane irin taimako kungiyarku ke ba mawaka?

kungiyarmu na taimaka wa sabbin mawakan da suka shigo ta hanyar ba su kwarin gwiwar yin kyakkyawan rubutu mai ma’ana ba tare da batsa ba ko zambo ko zagin wani, tare da dora su a kan turbar girmama na gaba da kamun kai da dai makamantan haka.
Ana kuma taimakon su ta fuskar kudi da makamantan haka.

Ana maganar cewa ba kwa ga miciji da Fati Nijar, ko haka abin yake?

Subhanallahi! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wallahi duk wanda ya fadi haka karya yake. Ni da Fati kud-da-kud muke, akwai soyayya a tsakaninmu mai karfi. Takan zo gidanmu ta gai
da iyayena, ni ma nakan je inda take mu kulla zumunci.

Ko akwai wani kalubale da kika fuskanta a lokcin da kika fara waka?

A lokcin da na fara waka yayana ya sanar da mahaifina, sai ya ce wakar me zan yi? Nan fa ya hana ni, to da ma daga makaranta nake biyawa wajen wakar.
Da ya ga na ki bari sai ya hana ni zuwa makarantar baki daya. Ni kuma saboda muhinmancin karatu sai na ga ba zan iya bari ba, har ya kai ga na yi yajin cin abinci.
Daga bisani ya hakura na koma makaranta na ci gaba da waka, wacce a yanzu ta zama sana’ata.

Wane salo kike dauka a wakarki?

A albam dina na Rabo-Rabo da jinsin mata, akwai wakar da na yi ta halin dan Adam sannan akwai wakar da na yi ta Auren Sunnah, yadda ake yin aure a musulunce, yadda a da ake da kunya a tsakanin maza da matan, da yadda ake bin tsarin neman aure ta fuskar neman yardar iyaye.
Sai kuma wakar da na yi ta Mace Tagari, ka ga duk namijin da bai samu mace tagari ba, yana cikin wani hali.

Na kuma yi waka a kan safarar mata, irin yadda ake dauko ’yan mata daga kauyuka ana sanya su ayyukan aikatau na bauta da yadda ake safarar mata zuwa kasashen ketare, ana sanya su karuwanci, ana gurbata masu rayuwa, da dai ire-irensu.

Wane alfanu kika samu a wannan sana’a taki ta waka?

To, alhamdu lillahi, na samu amfani da dama da ba za su misaltu ba sai dai na gode wa Allah a cikin wanna sana’ar ta waka ce na biya wa iyayena suka sauke farali, ni ma na je Hajji na sauke nawa faralin, a cikinta na gina gida na sanya iyayena, da dai sauran alfanu da ba zai yiwu na fade su duka ba.

A ina aka kwana a maganar aure?

E, to muna nan muna ta addu’a kuma muna so masu sauraronmu, masoyanmu su ci gaba da taya mu da addu’a, Allah Ya ba mu miji mafi alheri; mutum nagari.
Lokaci muke jira, muna fatan wannan jinkiri ya zame mana alheri, don ni babban burina in yi aure in gina makarantar Islamiyya, in sadaukar da ita ina kuma fatan cin ma wannan buri nawa matukar ina da sauran numfashi a duniya.
Daga: Jaridar Aminiya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button