Labarai
Ba Zamu Nunawa Duniya Hoton Dan Mu A Yanzu Ba, Har Sai Idan Ya Cika Shekara 18 – Zahra Buhari Da Mijinta Ta
Har ya zuwa yanzu babu hoton dan diyar shugaban kasa, Zahara Buhari da mijinta Ahmad Indimi da ya bayyana a shafukan sada zumunta, watakila wannan dalilin yasa shafin Northernblog dake dandalin Instagram ya saka wannan hoton na sama yake tambayar idan akwai me hoton dan ma’auratan ya fito dashi a gani.
Saidai a yayin da mutane keta bayyana ra’ayoyinsu akan wannan tambaya da Northerblog yayi, kwatsam sai ga mahaifin yaron me suna Muhammad, watau Ahmad Indimi ya bayyana cewa shi yana da hoton.
Jin haka yasa wata ta tambayi cewa to a nuna mana, saidai Ahmad yace, A yi hakuri sai ya cika shekaru 18.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com