Uncategorized

Abubuwan Da Ya Kamata Uwa Ta Koya Wa ‘Yarta Kafin Aure


Abin da ya sa na kawo wannan maudu’in shi ne, na ga wasu daga cikin iyaye suna da wata dabi’a, idan suna da yarinya mace ba su son koya mata komai. Sai a ga yarinya kamar wata sanda saboda ga ta nan dai, sai za a aurar da ita a yi ta kame-kame. Kuma sai a ga an makara a lokacin. Ko kunya ne ko nauyi ne, amma ke da ‘yarki, ya kamata ki zaunar da ita yau ki yi mata tambayoyi ko ki koya mata wasu abubuwa wadanda za su amfane ta cikin duniyarta da kuma lahirarta. Sai kin aurar da ita ta je ta yi ta aikata wasu abubuwa wanda shi kanshi mijin sai ya yi ta mamaki ballantana ‘yan uwansa.
Wajibi ne uwa ta tabbatar da cewa diyarta kin dora ta kan wannan:
*Addinin ta: Yanda za ta bautawa Ubanginta, yanda za ta tsarkake kanta a duk halin da ta tsinci kanta da sauransu.


*Tarbiyya: Wato girmama na gaba da ita, iya furuci ga duk wanda ta hadu da shi, wanda daga maganar ta ma za a san daga kalar gidan da ta fito, ba kibar ‘yarki ta yi ta magana babu kwaba babu nusarwa ba, idan kika ga ta furta wata kalma wacce kika ji ba ta dace ba, a matsayinki na wacce ta fita sanin rayuwa ki kwabeta sannan ki nuna mata wannan kalmar ba ta da kyau. Ki koya mata gaishe da manya, ta haka ne ko aure ta yi ba za kiji miji ya kawo karar ba ta gaishe da shi don ya mata laifi ba, ko ba ta girmama iyayensa da sauransu.


*Ki koya mata sanin darajar Dan Adam: Manya da kanana, talaka ko me kudi, nakashasshe ko kuma almajiri. Ki nuna mata ko wana mutum me daraja ne, kuma duk wanda ta gani a cikin kaskanci ko daukaka ba hakan yana nufin ya zamo abin wulakantawa ba. Ta hanyar haka ne za ki koya mata tausayi da taimakawa wanda ba su da shi da kuma rashin wulakanta kowa a cikin duniya, hakan zai sa ta rabu da girman kai ta gane ba ta fi kowa ba kuma kowa bai fita ba a duk inda ta tsinci kanta.

*Ki koya mata tsafta sosai: ki koya mata tsafta koda a kan kannenta ne idan tana da su, ta yanda ko ta haihu ba za ta sha wahalar kula da yaro ba, ko ba ta da su ki dinga koya mata, ki koya mata tsaftan jiki lungu da sako na jikin ‘ya mace yanda za ta gyara shi da tsaftan gida da sauransu. Ko ba ta son yin aikin gida wajibinki ne ki tsaya tsayin daka har sai ta kware da hakan, wata rana za ta gane kin mata gata babba.

*Ki koya mata ado na mutunci: Yanda za ta dinga ado na mutunci kuma tare da nuna mata adon gidan miji wanda za ki nuna mata shi sai ta yi aure za ta dinga yinsa. Ina nufin ‘yarki budurwa, domin rashin sabawa yarinya da ado yana sawa idan ta je gidan miji ta kasa yi, idan aka ce ado ana nufin gyaran fata, lalle, gyaran gashi da sauransu, ba ado na fitar da tsaraici ba.

*Ki koya mata girki: Idan tana gida ba makaranta ki ba ta girki ta yi, ko idan ta dawo daga makaranta ta huta, idan da wani abu da baki karasa ba ki ce ta zo ta yi maki, a hankali za ki ga tana koyon girki, don girki ba a koyon sa dare daya.

*Ki dinga ba ta labarin halin samari da yanda za ta tsallake tarkonsu da yanda za ta kare mutuncin kanta da budurcinta, ki dinga sa ido sosai gami da rokon Allah sosai.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button