Kannywood
Abinda Yake Damuna A Yanzu Duniya Daya ne – Inji Sadiya Gyale
Advertisment
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Sadiya Gyale, ta ce masu yin amfani da sunanta suna yada labaran karya suna matukar bata mata rai.
Ta bayyana hakan ne a shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa wanda aka gabatar ranar Juma’a da almuru kan “Yadda za a magance yaduwar labaran karya.”
A watan Yuli ne aka rika yada jita-jita a kafafen sada zumunta cewa jarumar ta mutu a asibitin Malam Aminu Kano da ke arewacin Najeriya.
“Tun da nake ban taba bude Facebook ba amma yanzu idan ka shiga manhajar za ka samu account biyar ko sama da haka suna amfani da sunana, kuma abin yana bata min rai saboda wasu ma sai ka ga sun shiga roko.
“A lokacin azumin da ya wuce na je Saudiyya sai wani ya rika amfani da sunana a Facebook yana cewa wai na je wani wuri kudi sun yanke min don haka a taimaka min da kati na dubu kaza. Gaskiya yadda ake amfani da sunana ana bata min suna yana damu na matuka.”
Abin da ta fada wa BBC lokacin da aka ba da rahoton rasuwar ta
Sadiya ta shaida wa BBC cewa, ita dai tana zaman-zamanta da lafiyarta, sai kawai taga ana ta kiranta a waya ana tambayarta ko lafiya don ga labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta.
Ta ce tun tana daukar abin kamar wasa, sai kuma ta ga cewa lallai an yada labarin cewa ta mutun.
Ta ce labarin mutuwarta ta da aka yada ya sa masoyanta da dama cikin tashin hankali, domin kuwa wasu daga cikinsu ko baccci kasa yi suka yi, wasu kuma a ranar ko abinci ba su iya ci ba inji ta.
Sadiya ta ce, ita agaskiya labarin sam bai dame ta ba, don kuwa a ranar ma bacci ta yi har da mun shari, domin ta san cewa dukkan mai rai mamacine wata rana.
Jarumar ta ce wadanda suka mutu ba gaggawa suka yi ba, haka wadanda suke raye ma ba jinkiri suka yi ba, fatan ta Allah ya sa ta cika da kyau da imani.
Sadiya Gyale, ta ce a gaskiya irin yada wadannan labarai na karya sam ba dai-dai ba ne a cikin al’umma musamman musulmai.
Ta ce “A gaskiya duk wanda ko wadda ta shirya wannan labari, to ta daukarwa kanta ko kansa babban alhaki, kuma ba bu wata riba da mutum zai samu a kan hakan”.
Jarumar ta ce duk wanda ke fadar wane ya mutu ko wance ta mutu a hali karya ne, to ai Allah ne kadai ya san gawar fari, kuma ba mamaki ma shi mutumin da ke yada irin wannan labarin shi ke kusa da rami.
@BBChausa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com