Labarai

‘Yan Luwadi Da ‘Yan Madigo Sun Jaddada Goyon Bayan Su Ga Atiku Abubakar.


Daga Haji Shehu 

………. Cikin sati 12 da kama aiki muke bukatar a halatta auren jinsi a Najeriya – Rokon Lesbian, Gay, Bisexual, and Transgender (LGBT) ga Atiku Abubakar.

A daidai lokacin da zaben 2019 ke gabatowa, wata kungiya dake kare hakkokin ‘Yan Madigo da Yan Luwadi mai suna Lesbian, Gay, Bisexual, and Transgender (LGBT) ta jaddada goyon bayanta ga dantakarar Shugaban kasa na jam’iyar PDP. 

A cewar kungiyar, Atiku Abubakar shine dantakara daya tilo da zai kula da hakkoki da muradun dukkanin yan Najeriya. Kungiyar ta soki gwamnatotin da suka shude da kuma gwamnatin da take kan mulki, da cewar ta takewa yan Luwadi da yan Madigo hakkokin su ta hanyar kafa dokokin da suka haramta auren jinsi tare da sanya zaman gidan fursuna na shekaru sama da 14 akan duk wanda aka kama  da laifin Luwadi ko Madigo.

Shafin jaridar Today ya nakalto LGBT na cewar “A wata mai kamawa zamu hada kan membobin mu domin tabbatar da ganin Atiku ya zama shugaban kasa kuma ya kawarda dokar hana auren jinsi cikin sati 12 da kama aiki a matsayin shugaban kasa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button