Sports

Sarkin Makkah Na Shirin Siyan Manchester United

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa Yarima Muhammad Bin Salman na kasar Saudiyya zai siyi ya na son siyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United idan har mamallakanta zasu siyar.

Rahoton ya bayyana cewa yarima Bin Salman ya na son ya siyi kungiyar ne gaba daya ko kuma ya siyi wani bangare na iyalan Glazer, wadanda sukafi kaso mafi tsoka a kungiyar.
Yarima dai ya na son Manchester United ta cigaba da goga kafada da kafada da abokiyar hamayyarsu wato Manchester City wadda itama larabarawa ne suke rike da ita.
Sai dai kamar yadda rahotanni suka bayyana, iyalan Glazer, basu da sha’awar siyar da kungiyar kuma zasuyi iya yinsu domin ganin basu siyar da kungiyar ba.

Rahotanni dai sun nuna cewa iayalan Glazer, masu kungiyar zasuje wani taro kasar Saudiyya a sati mai zuwa kuma ana ganin a wajen taron Yarima Bin Salman zaiyi musu tayin siyan kungiyar.
Masu kungiyar dai sun siyi kungiyar ne a tun a shekara ta 2005 akan kudi fam miliyan 850 sai dai kawo yanzu ana ganin kungiyar zata kai fam biliyan uku.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button