Kannywood

Dan KUKA A BIRNI Da TAQADDAMA sun Fita A Kasauwa Ku nemi Naku

A y’an kwanaki da suka shude jarumi Adam A. Zango tare da wasu masu ruwa da tsaki a shirin barkwanci na Dan Kuka a Birni suka fara bada sanarwar fitar da film din a kasuwa bayan kwashe sati sama da biyu ana haska shirin a Cinema.

Dan Kuka A Birni idan baku manta ba cigaba ne na Dan Kuka inda a wannan Zangon Ado Isah Gwanja wanda ya taka rawar Dan Kuka ya fita daga kauyensu ya shiga birni inda ya hadu da wata waki’ar…
Ku nemi film din a kasuwannin kusa daku domin more wa idanuwanku tare da samun nishadi yayin kallo, kamar yadda masu shirin suka bayyana cewa an yi film dinne musamman saboda masu ciwon hawan jini da damuwa.
An bayyana manyan matasan jaruman Kannywood a cikin shirin:
Ado Isah Gwanja
Adam a. Zango
Zahradeen Sani Owner
Horo dan Mama
Falalu A. Dorayi
Fati Abdullahi Washa
Da sauransu.

A kwanaki cewa wannan shiri TAQADDAMA yana dab da fitowa kasuwa kamar yadda kamfanin JS INUWA INTERNATIONAL LTD ta bada sanarwa.
Tare da Dan Kuka a Birni suka fita kasuwa. Shima wannan shiri ne mai ma’ana dauke da sakonni da dama wanda ya dace duk dan Nigeria ya kalla bisa muhimmin sakon da yake dauke dashi. Fitattun jarumai ne kamar su:
Aminu Aliyu Shariff
Ali Nuhu
Baballe Hayatu
Abba El-Mustapha
Rabiu Rikadawa
suka bada gudunmawarsu wajen ganin shirin ya zo gareku cikin nasara.

©Movie Week NG

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button