Kannywood

Dalilin Da Yasa Na Saya Suma Ali Nuhu N500,000 Ya Aske kansa – Alhaji Sheshe

Fitaccen furodusa a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Alhaji Mustapha Ahmad wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe ya ce ya biya shahararren jarumi, Ali Nuhu Naira dubu 500 ne don ya aske gashin kansa saboda rawar da jarumin zai taka a fim dinsa mai suna ‘Kazamin Shiri’ tana bukatar jarumin sai ya aske gashin kansa don fim din ya samu karbuwa a wurin masu kallo.

Alhaji Sheshe ya bayyana haka ne a tattaunawa da Aminiya ta kafar sadarwar WhatsApp.
Furodusan ya ce babu jarumin da ya dace ya fito a fim din fiye da Ali Nuhu, kuma ana bukatar da sai ya yi aski, shi ya sa ya biya kudin don jarumin ya aske gashin kansa.
Duk wanda ya san Ali Nuhu ko yake kallon fina-finansa fiye da shekara 10 ya san shi da wani salon aski da ake kira ‘FKD’, duk irin fim din da zai fito jarumin ba ya yarda ya asken gashin kansa.

Idan ba a manta ba ko fim din Barde da ya fito wanda ake bukatar ya yi askin kwal-kwabo ma bai yi askin ba, face an kira wani mai yi wa ’yan fina-finan Kudancin kasar nan kwalliya da ake kira Akeem, inda ya yi dabarar da ta nuna kamar an yi wa Ali Nuhu aski kwal-kwabo.
Ya ce, “Saboda yanayin fim din Ali Nuhu talaka ne, kuma a yanayin rayuwarmu ba za ka taba ganin talaka da askin ’yan gayu ba, don haka labarin yana bukatar ganin abu a zahiri ne, sannan rol din shi ya kira shi ya sa na ga ya dace in sayi gashin kan nasa ya yi mini aski.
Kuma na ji dadi da ya amince da hakan, domin a wasu lokuta ya ki yarda ya yi askin don da wadansu sun nemi ba shi kudi.”

A yanzu dai tuni aka fara daukar fim din ‘Kazamin Shiri’ a Kano, inda za a shafe kwana 10 ana daukarsa.
Jaruman cikin shirin fim din sun hada da Ali Nuhu da Aminu Shariff (Momo) da Rabi’u Rikadawa da Fati Washa da Bilkisu Shema da Inteesar el-Fallata da Hajara Usman da sauransu.

Ibrahim Birniwa ne ya tsara labarin, Alhaji Sheshe ya shirya shi, inda Sunusi Oscar 442 ya ba da umarni.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button