Labarai

Atiku Ya Fi Buhari Cancantar Zama Shugaban Nijeriya –Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana dan takarar jam’iyyar PDP a zabukkan shekarar 2019, wato Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da ya fi shugaba Buhari cancantar zama shugabantar kasar nan.

Wannan kalaman sun zo ne bayan wata ganawar sirri da ta gudana a yau tsakanin tsofaffin abokan hamayyar siyasa biyu, duk da shaharar da suka yi a matsayin abokan hamayya, a yau Cif Obasanjo ya bayyana goyon bayanshi dari bisa dari ga takarar Atiku Abubakar din.
Wadanda suka halarci ganawar sirrin sun hada da, shugaban jam’iyyar PDP ta kasa Uche Secondus, tsohon gwamnan jihar Ogun Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Kuros Ribas Liyel Imoke, Cif Bode George, Rabaran Mathew Hassan Kukah, Sheikh Ahmad Gumi, Bishof Oyedepo da Ayo Adebanjo na kungiyar Afenifere.

Obasanjo da Atikun sun cimma matsaya, inda suka amince su ajiye bambancin da ke tsakaninsu, don goya wa Atikun baya ya kada Buhari daga mulkin kasar nan in Allah ya kaimu zabukkan shekarar 2019.
Obasanjo ya na ganin Atiku Abubakar ya fi shugaba Buhari sannin tattalin arzikin kasar nan, don haka yakamata ya goya wa Atikun baya don a samu a ceto tattalin arzikin kasar da ya shiga halin kakanikayi a karkashin shugabancin Buhari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button