Kannywood

Harka Fim Tayimin Goma Ta Arziki -inji Al-Ameen Buhari

Al-Ameen Buhari yana daya daga cikin manyan jaruman masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood, a hirar da Aminiya ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ya fara harkar fim da kalubalen da yake fuskanta a masana’antar da yadda ya sa aka sauke masa Alkur’ani kafin ya shiga harkar fim, inda ya ce fim ya yi masa riga da wando:

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Al-Ameen Buhari, an haife ni a garin Jos, na yi karatun boko da na addini daidai gwargwardo. Na yi karatun kur’ani da hadisai a Lafiya da ke Jihar Nasarawa. A bangaren karatun boko kuwa na tsaya a sakandare ne, kafin in shiga harkar fim ina sana’ar tukin babbar mota ce, daga baya na fara harkar fim. Ina da mace daya da ’ya’ya biyar, inda na aurar da ’yata ta farko kuma a yanzu nake da jika.

Me ya ja hankalinka ka fara harkar fim?

Babban abin da ya ja hankalina na fara harkar fim shi ne, kamar yadda na gaya maka daga cikin tarihina, wato na yi karatun Muhammadiyya sosai, don har nakan fadakar da al’umma, ma’ana nakan yi wa’azi. A lokacin da harkar fina-finan Hausa ta fito sai na ga cewa wata hanya ce mafi sauki da mutum zai iya wa’azantarwa.
Idan ka kalli shirin fina-finanmu za ka ga daidai suke da wa’azantarwa, za ka ga mutum ya dauko rayuwa wacce ba hanyar Allah ba, daga karshe ya ga sakamako tun a duniya, daidai yake da malami ya ce ka bi Allah da Manzonsa (SAW), ka kyautata za ka ga sakamako mai kyau.
Ka zauna da makwabtanka da iyayenka za ka sakamakon hakan tun a duniya, haka a fim za ka mutum ya fito yana shaye-shaye ko bin mata ko kashe-kashe, za ka ga ko dai ya tuba, ko kuma karshensa ba zai zo da kyau ba, hakan sai ya sa na ce in na shiga harka fim to zan ba da gudunmawata wajen aika sakon zama lafiya da bin Allah da kyautata wa makwabta da sauransu.
Wane kalubale ka fuskanta lokacin da ka yi yunkurin shiga harkar fim?
A gaskiya ban fuskanci wani kalubale da zan ce ya takura wa rayuwata ba, dalili kuwa shi ne a shekarun baya kafin in shiga harkar zan iya tunawa wata rana ana nuna wani fim mai suna ‘Nazari’ a gidan silima na Kwararafa a nan Jos, a fim din akwai Ali Nuhu da Kumurci da Fati Muhammad da Abida Muhammad da sauransu, wanda ya shirya fim din shi ne Yusuf Khalid. Shi kuma abokina ne, to fim din ya ba ni sha’awa, domin muna ta kallon fina-fina Indiya, muna kallon na Turai, a ranar kuma na kalli na Hausa kuma ya yi mini dadi, sai na je shagonsa bayan na kammala kallon fim din na ce masa duk lokacin da zai sake yin wani fim to ya sanya ni a ciki, domin ina da sha’awa. Sai ya ce idan zai sake wani to zai sa ni a ciki.
Haka na rika matsa masa, sai ya zamana na hadu da wani bawan Allah da yake neman mota za ta yi jigilar ’yan fim zuwa wurin daukar wani fim. Sai na ce masa ai dama ina da ra’ayin fim muka je wurin inda a nan na hadu da Salisu Mu’azu kanen Sani Mu’azu, bayan na yi masa magana sai ya ce mini zai shirya wani fim mai suna ‘Fargaba’. Da aka zo shirya fim sai aka fara gwada ni, sai ya ga abin nawa ya yi kyau, sai ya yi mini fatan alheri.
Kudin da ya biya ni a wancan lokacin sai na ce tun da wannan kudi ina da hanyar cin abincina, wannan wata sabuwar hanya ce, to bari na sa a roka mini Allah, in ba da sadaka da wannan kudi nawa na farko domin Allah Ya zama gata a tafiyar. Aka sauke mini Al’kur’ani na yi sadaka da niyyar wannan sana’a da na sa ta niyyar fara fina-finai, to Allah Ya sa ta daure mini gindi, don in kai wani matsayi. Kuma alhamdulillahi na yi fina-finai masu muhimmanci, ina kuma jin dadinsu da kuma alfahari da su, saboda sakonnin da suka isar.

Ko ka san adadin fina-finan da ka yi kawo yanzu?

Magana ta gaskiya idan na hada kaina da manyan jarumanmu zan iya cewa ban yi wasu fina-finai masu yawa ba. Dalili da ban yi da yawa ba, saboda a nawa tsarin ba na karbar fim din da ba ya da ma’ana. Sa’annan kuma ba na yarda in yi aiki da daraktocin da ba za su tsaya su yi aiki mai kyau ba. Daraktocin da ba su yarda da aikinsu ba, za ka ga ba sa ma nemana.

A cikin fina-finan da ka yi zuwa yanzu wanne ka fi so, kuma me ya sa?


Zan iya fitar da fina-finai kamar uku, har kwanan gobe ina alfahari da su. Da farko akwai wani fim mai suna ‘Fari Da Baki’ na kamfanin darakta Aminu Saira, na ji dadin fim din saboda yadda sakon ya isa ga al’umma. Fim ne kan zamantakewar aure, na kasance ina da mace da mahaifiyata ba ta kaunarta, da ta zo sai ta ga matata da ciki, sai ta ce cikin ba nawa ba ne, domin zaman bai kai a samu ciki ba.
A fim din sai na biye wa mahaifiyata na ce cikin ba nawa ba ne, na sake ta, ta haifi dan, ni kuma na sake wani aure, matata kuma ta zo mini da dan da ba nawa ba, kuma na rungume shi. dana har ya girma na yi rashin lafiya aka kai ni asibitin da yake aiki, wato bayan ya zama likita ke nan, shi kuma wancan dan da ba nawa ba ina matukar sonsa, amma yana gana mini azaba.
Sai fim din ‘Ahlil Kitabi’ na Adam A Zango, fim ne na tarihi, inda yake da shigen kissar Annabi Yusuf (AS), na fito a cikin gefen ’yan uwan Annabi Yusuf, inda ni kuma na hau rol din kamar Yahuza, na rika gana wa Zango azaba, ina so fim din saboda sakon da ya isar.
Sai fim na uku wato ‘Azal’ na kamfanin 3SP wanda muka yi shi a nan Jos, na fito a matsayin azzalumin dan sanda, ga gaskiya amma saboda an ba ni cin hanci, sai in shafa wa idona toka, na rika gana wa mai gaskiya azaba, in yanka masa kazar wahala.

Yanzu za a iya cewa burinka ya cika a Kannywood?

Burina yana kan cika,
zan iya cewa a cikin buri 10, to na samu bakwai, ina harin na takwas. A halin da ake ciki a yanzu ina da mata da ’ya’ya, cina da shana da suturata haka nasu, kula da lafiya da makarantarsu duk muna samu ne daga wurin Allah ta karkashin Kannywood. Na hau mota don alfarmar fim, na kwana a wuri mai kyau don alfarmar fim, fim ya yi mini riga da wando, shi nake yi yau da gobe. Abin da ya rage mini shi ne in mallaki gida nawa, in je aikin Hajji, sannan kuma in kara aure.


Zuwa yanzu wane kalubale kake fuskanta a Kannywood?

kalubalen da nake fuskanta a Kannywood ba ni kadai ba ne, mafi yawan ’yan fim suna fuskanta wannan kalubale, wato matsalar lalacewar kasuwa, ta taba kowa a Kannywood, wadda muna rokon Allah Ya kawo mana tallafi. Kuma muna rokon gwamnati ta kawo mana tallafi. Babu wanda ya san adadin wadanda suke ci a Kannywood, dubban mutane suke cin abinci a Kannywood, to ka ga an taimaki gwamnati wajen rage marasa aikin yi. Misali idan furodusa zai shirya fim na kwana bakwai, to za ka samu sama da mutum 150 suna cin abinci a karkashinsa, don haka ya kamata gwamnati ta taimaka wa ’yan fim.
Ya kamata gwamnatin Buhari ta taimaki ’yan fim saboda sun ba ta gudunmawa sosai, ta gyara mana masana’antarmu, ta ba mu jari, sannan ta yi mana yaki da masu satar fasaha.

Daga karshe wane sako kake da shi?

Wannan ya shafi abubuwan da suke faruwa a jihata, wato Filato da kuma karamar hukumata ta Jos ta Arewa, abubuwan da suke faruwa suna damuna, kuma babban abin yake kawo rashin ci gaba shi ne rashin zaman lafiya. Tun daga lokacin da aka kafa dimokuradiyya a 1999 zuwa yanzu mun yi gwamnoni uku, Dariye da Jang, yanzu kuma Lalong, ba mu taba samun Gwamnan da yake kokarin tabbatar da zaman lafiya kamar Lalong ba.
Ni ba dan siyasa ba ne, don haka idan Lalong bai yi kokari ba, to ba zan yabe shi ba, don haka ya kamata Musulmi da Kiristan Jihar Filato mu hada kai, sannan mu taimaka wa Lalong don a samu zaman lafiya. Zaman lafiya zai kawo mana ci gaba sosai, kakan iya fita ka yi harkokinka ka dawo ba tare da dar-dar ba. Amma idan babu zaman lafiya hakan ba zai yiwu ba. Don haka idan aka yi tashin hankali babu abin da yake biyowa baya face talauci, don haka mu zauna lafiya da junanmu.
©aminiya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button