Labarai

An Samar Da Kotun Kare Hakkin Masu Amfani Da Yanar Gizo A Kasar Chana

 Daga Wakiliyarmu Amina Yusuf Ali.

 A yau Talata ne kotun da kasar Cana ta Samar a garin Hangzhou  ta fara aikin sauraren kararrakin da suka shafi harkar yanar gizo. Kuma za a dinga yin shari’ar ma  ta yanar gizo.

 Ranar Lahadin da ta gabata ne kasar Cana ta yanke shawarar ware kotun shar’iar yanar gizo ta zama daban da ta sauran shari’u.  Wannan kotu za ta saurari kararraki da korafe-korafen da da suka shafi harkar yanar gizo. Kamar abinda ya shafi rigima a kan satar fasaha da harkar kasuwancin da ake kullawa ta yanar gizo, da makamantansu.

 Kuma aka Bude kotun a garin Hongzhou saboda gari ne Wanda yake da masana’antu da kamfanonin na’ura mai kwakwalwa da dama. Kuma shari’u Suna Neman su yi Wa kotun yawa domin ko a shekarar baya ma an samu kararraki har guda 10,000, wadanda suke da alaka da kasuwancin yanar gizo da makamantansu. Don haka aka ga ya kamata a samar da kotun yanar gizo.

 Wacce za ta saurari kara, kuma ta yi shari’a, sannan ta yanke hukunci a yanar gizo. Wani Farfesa daga jami’ar Beijin ta kasar Cana mai suna, Xie Yongjiang ya bayyana wa CGTN cewa ya zama dole a Samar da kotun saboda yadda fasahar zamani ta yanar gizo ta shiga rayuwar mutane, dole a iya samun sabani.  Kotun ta yi alkawarin kare hakkin duk wani ma’abucin yanar gizo. A halin yanzu dai har ani tura wa wannan sabuwar kotun kararraki har guda 200 a jiya litinin Wadanda ta fara aiki a Kansu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button