Labarai

Yadda limami Ya Cigaba Da sallah Yayin Da Girgazar kasa Ta Riske su a cikin masallaci (kalli bidiyo)

Girgizar kasar ta faru ne daren ranar lahadi 5 ga watan Agusta inda kimani mutane sama da 82 suka rasa rayukana su yayin da wasu da dama suka rasa muhallin su

Al’ummar tsibirin Lombok dake kasar Indonesiya sun gamu da fargaba yayin da wata girgizar kasa mai nauyin maki 6 ta riske su.
Girgizar kasar ta faru ne daren ranar lahadi 5 ga watan Agusta inda kimani mutane sama da 82 suka rasa rayukana su yayin da wasu da dama suka rasa muhallin su.

Kamar yadda labarai suka nuna adadin mutane da suka rasa rayukan su ya kai 96 kuma sun riski ajalin su ne sakamakon ginin gidagen da ya rufta a kan su.

Wani abun da ya dauki hankali shine bidiyon wani limami dake jagorantar sallar Ishai yayin da lamarin faru. A cikin bidiyon limamin bai katse sallah ba yayin da wasu daga cikin mamun da yake jagoranta suka tsere don neman tsira.

bidiyon dai ya mamaye shafuka da kafofin watsa labarai inda da dama ake yabon tirjewan da limamin yayi duk da girgizar kasa dake faruwa.

A wata rahoto da kamfanin dillancin labarai ta AFP ta ruwaito, wani shaidar gani da ido ya sanar cewa a dai dai lokacin da lamarin ya faru ana sallar isha’i a cikin wata masallaci mai suna Jabal Nur dake yankin kauyen Lading-lading na tsibirin.

Yace limamin ya gudu ana sallah inda suma mamun suka bi sahun shi. Bayan haka hukumar dake ceton rayuka sun tabbatar da cewa mutum uku sun rasu a cikin baraguzan masallacin.

Tsibirin ombok tana daya daga cikin manyan cibiyoyin addinin musulunci na kasar. Tafi ko wani yanki na kasar yawan musulmai a kasar.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button