Mawaki Hausa Na Arewa Dezell Ya Saki Matarsa Aisha
Shahararren mawakin hausa Hip hop Dezell wanda ya yi wakar Girma da kuma Ubansu, wakokin da suka dade ana yayin su arewa, ya sake zuwa maku da wata sabuwar bidiyonsa da suka yi da da fitaccen mawakin kudadancin kasar nan Koredo Bello,sun sanya wa wakar suna Aisha.
Tun daga lokacin da kafaffen sada zumunta na twitter da kuma instagram suka karrama mawakin da alamar tauraro a shafinsa ya zama kusan shike rike da farfajiyar wakar Hausa Hiphop. Dezell yana daya daga cikin manyan mawakan da kan iya hada Hausa tare da Turanci a waka kuma su tafi yadda ya kamata. A halin da ake ciki yanzu Dezell shike kara daukaka farfajiyar Hausa hip hop, domin kuwa har yanzu ba a samu wani mawaki dake kokarinsa ba.
Ibrahim Rufa’I wanda aka fi sani da Dezell an haifeshi ne a Jihar Michigan kasar Amerika a, iyayensa sun dawo da shi Nijeriya yana da shekara biyar, daga bi sani kuma ya koma USA ya yi karatun degree dinsa a can, ya fara harkan waka da wasan fim tun akasar Amurka inda ya bayyana a fina finan su da dama, daga bisani ne kuma ya yanke shawara ya dawo Nijeriya don ci gaba da harkokinsan tare da kuma waka.
Ya yi wakoki da dama a kasar Amurka, sunan Midtape dinsa na farko “Bault” a cikin wannan Midtapes ya sa shahararrun mawaka daga ciki akwai Kuinn da Yung6id da Alicom da Fela da kuma Maaka da dai sauransu.
Cikin kwanankin nan Dezell ya kara mikewa tsaye gurin ganin ya kara daukaka rayuwar wakokinsa,watan baya da ya wuce mawakin ya saki wata waka mai taken Aisha wanda suka yi tare da Koredo Bello, wakar ta samu karbuwa sosai, inda ya samu kyaututtuka da dama a kan wakar Aisha, inda ya yanke shawarar ya yi wakar a bidiyo.
To a satin nan ne Dezell ya saki bidiyon wakar Aisha, bidiyon wakar ya samu dauka mai kyau inda kwararren darakta mai suna Philm City flicks ya bada umarni, an dauki bidiyon ne a Legas.
Sannan kuma bayyan ya saki wakar Slay Mama da One Time, ke karar sanarwa cewa, nan bada jimawa ba zai kara sako sabon bidiyo, sai dai bai fada mana suna wakar ba, ya ce, wakar za ta iya zama sabo a gurin al’umma.
Dezell ya taimaka kwarai gurin ganin ya daukaka kananan mawaka a Nijeriya musamman nan Arewa.
A saboda haka idan kana daga ciki masu sha’awar wakokin Hip hop to lallai ya kamata ka mallaki sabon wakar nan mai suna ‘Aisha’ wadda shaharrarun mawaka Deezell da Korede Bello, suka buga, muna kuma fatan wannna zai zama kamar somin tabi na sabbin wakoki da zasu ci gaba fitowa daga wadannan zakakuran mawakan wannan zamani namu wadanda suka zama abin koyi ga matasan mawaka masu tasowa a kasarmu Nijeriya.
Sources:presshausa.com