Labarai
DA DUMIDUMINSA WATA SABUWA: Nan Da Awa Daya Ake Sa Ran Kwankwaso Zai Bar APC
Rahotanni sun nuna cewa a yau Laraba Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso zai yi bankwana da jam’iyyar APC zuwa PDP, kamar yadda majiyarmu ta Daily Trust ta rawaito.
Da yawa daga cikin na hannun daman Sanatan ne suke ta yada shirin ficewar Sanatan daga APC a shafukansu na sadarwa.
Daya daga cikin na hannun daman Sanata Kwankwaso, Hajiya Binta Spikin, na daga cikin wadanda suka yada sanarwa shirin Sanatan na yin hannun riga da APC, inda a wani sashe na rubutun nata ta bayyana cewa “nan da karfe biyu na rana za a yi rashin wani jigo a wata jam’iyya”.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Allah ya kyauta amn