Kannywood

Ban Taba Cin Fuskar Buhari Ko Zakzaky Ba A ‘Facebook’, Inji Ummi Zee-zee


Daga Aliyu Ahmad

Tsohuwar jarumar finafinan Hausan nan, Ummi Ibrahim wadda aka fi sani da Ummi Zee-zee ta karyata labaran da suke yawo a kafafun sadarwa musamman facebook, inda ake nuna cewa tana cin zarafin shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu malamai irin su Sheik Ibrahim Zakzaky.

A yayin tattaunawar ta da RARIYA, Zee-zee ta kara da cewa “tunda nake a ban taba yin wani rubutu da sunan cin fuska ga shugaba Buhari ba, kawai wasu ne ke amfani da sunana a shafin sada zumunta suna cin zarafin shugabanni”.

Ummi Zee-zee ta kuma kara da cewa ba ta da alaka da zagin da ake yi wa jagoran mabiya Shi’a Sheik Ibrahim Zakzaky, domin ta dauke shi a matsayin babban malami a kasar nan. Don haka ba ta ga dalilin da za ta ci fuskar sa ba. Kawai wasu ne suke amfani da sunanta domin bata mata suna.

Zee-zee ta kuma jawo hankalin kakakin kungiyar harkar musulunci (IMN) wato Malam Musa Ibrahim da ya sani cewa ba ta nasaba da wannan cin fuskar da ake rawaitowa a kafafun sadarwa cewa tana yi jagoransu Sheik Zakzaky.

Haka kuma Zee-zee ta ja hankulan jama’a musamman mabiya shafukan sadarwa da su nisanci duk wani rubutu na cin zarafin shugaba ko wani Malami da sunanta, domin ba ita ba ce.

“Wallahi duk wadannan rubuce-rubuce da ake yi a shafukan sadarwa na cin zarafin Buhari ko Zakzaky da ma wasu manya a kasar nan ba ni ba ce, kawai ana yi ne domin a bata min suna”, inji Ummi Zee-zee.

Idan masu karatu za su iya tunawa, sau da yawa akan samu wasu shafuka dauke da sunan tsohuwar jarumar finafinan Hausan, inda ake rubutun batanci ga shugaba Buhari ko wasu Malamai da sauran masu fada a ji. Wanda kuma jama’a suke zaton kamar ita ce ke yi. 

Saida a yau Zee-zee ta fito ta nesanta kanta da irin wadannan shafuka na bogi da suke yin amfani da sunanta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button