Ban Mutu Ba Ina Nan Da Raina -Inji Tsohuwar Jaruma Sadiya Gyale
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Sadiya Gyale, ta karyata labarin mutuwarta da aka yada a kafafan sada zumunta.
Sadiya ta shaida wa BBC cewa, ita dai tana zaman-zamanta da lafiyarta, sai kawai taga ana ta kiranta a waya ana tambayarta ko lafiya don ga labarin da ke yawo a kafafan sada zumunta.
Ta ce tun tana daukar abin kamar wasa, sai kuma ta ga cewa lallai an yada labarin cewa ta mutun.
Ta ce labarin mutuwarta ta da aka yada ya sa masoyanta da dama cikin tashin hankali, domin kuwa wasu daga cikinsu ko baccci kasa yi suka yi, wasu kuma a ranar ko abinci ba su iya ci ba inji ta.
Sadiya ta ce, ita agaskiya labarin sam bai dame ta ba, don kuwa a ranar ma bacci ta yi har da mun shari, domin ta san cewa dukkan mai rai mamacine wata rana.
Jarumar ta ce wadanda suka mutu ba gaggawa suka yi ba, haka wadanda suke raye ma ba jinkiri suka yi ba, fatan ta Allah ya sa ta cika da kyau da imani.
Sadiya Gyale, ta ce a gaskiya irin yada wadannan labarai na karya sam ba dai-dai ba ne a cikin al’umma musamman musulmai.
Ta ce ‘A gaskiya duk wanda ko wadda ta shirya wannan labari, to ta daukarwa kanta ko kansa babban alhaki, kuma ba bu wata riba da mutum zai samu a kan hakan’.
Jarumar ta ce duk wanda ke fadar wane ya mutu ko wance ta mutu a hali karya ne, to ai Allah ne kadai ya san gawar fari, kuma ba mamaki ma shi mutumin da ke yada irin wannan labarin shi ke kusa da rami.
Sadiya ta ce, tana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na gangami a kan masu yada labaran karya musamman a kafafan sada zumunta.
A kwanakin baya dai gwamnatin Najeriya ta bullo da shirin yaki da labaran kanzon kurege, amma kuma har yanzu a iya cewa ba a rabu da Bukar ba domin kuwa har yanzu ba a fasa ba.
Wacece Sadiya Gyale?
Tana daga cikin jaruman fina-finan Kannywood da suka yi fice musamman a tsakanin shekarun 2000 zuwa 2012.
Ta fito a fina-finai da suka yi fice kamar Balaraba da Ikram da Kugiya da Tutar So da Kishiya ko ‘yar uwa da kuma Kauna.
Tayi aure a shkerar 2015, amma kuma daga bisani sun rabu da mijin.
Bata fitowa a cikin fina-finai a yanzu.
Ta fito a fina-finai tare da jarumai kamar Ali Nuhu da Marigayi Ahmad S Nuhu da Aminu Shariff Momoh da dai sauransu.