Kannywood

Abincin wani Gubar wani : Har Suma Nayi Lokacin Daukar Fim Din Badali – Inji Jarumi Tijjani Asase

Advertisment

TIJJANI ASASE wanda a da aka fi sani da suna ‘Damisa’, daya ne daga cikin shahararrun jarumai a masana’antar fim ta ‘Kannywood’. Ya taka muhimmiyar rawa a harkar fina-finai da dama, wanda tunda fim din Hausa ya fara haskawa kawo yanzu shi ma tauraruwarsa ba ta tusashe ba, domin ko yau ko gobe ana ganinsa a fin-finai. Ya yi shuhra wajen fitowa a gurbin da ba kowa ke iya yi ba, wato bangaren masu alkata manyan laifuka amma a fim. Tun ana damawa da shi a matsayin saurayi, har a yanzu ya kai matsayin yana fitowa a matsayin uba, wannan ya nuna matukar jajircewarsa cikin wannan sana’a. A wannan hirar ya bayyana wa wakiliyarmu JUMMAI IBRAHIM abubuwa da dama game da rayuwarsa a cikin fim da kuma wajen fim ciki har da ra’ayinsa na cewa, shi zai iya auren jarumar da ta yi suna a fim in har ya samu wadda ta dace da shi. Ga yadda hirar ta kasance kamar haka:
Muna so ka fara da bayyana cikakken tarihin rayuwarka…
Sunana Tijjani Abdullahi (Asase). An haife ni a unguwar Dandago Karamar hukumar Gwale cikin birnin kano, na yi makarantar Firamare a gwale, na yi sakandire duk a Gwale, amma ban samu damar kammalawa ba.

Mene ne dalilin da ya ja ra’ayinka ka shiga harkan Fim?

A bin da ya ja ra’ayina na shiga harkar fim shi ne mu’amala da su da nake yi ita ce tai sanadiyyar kasancewa ta acikinsu sakamakon bude ofis da Ado Ahmad ya yi a Unguwarmu ni ne na farko a yara da yake aika duk a yaran unguwarmu, shi ya sa na kasance a cikinsu daga nan na tsinci kaina a cikin ‘yan fim.

Ta yaya kake kallon masana’antar fina-finan hausa a yanzu?

Wata masana’anta ce da ake yin arziki a cikinta, amma su wadan da suke cikinta yanzu sun mai da, ita ta cin abinci duk in da za ka shiga ka kalli masu yin fim a duniya yanzu za ka ga masu kudi ne, amma ban da na Kannywood. Su iyakacinsu su samu na cin wake da shinkafa, Ka sayi gida, Ka sayi mota ka sa kaya ka fito kana yi wa kowa kallon matsiyaci, alhalin baka da miliyan talatin a aajiyar kudinka.

Wane irin kalubale ka taba fuskanta a harkar tun da ka fara?

Kalubalen da na taba fuskanta Shi ne, ranar da Ali Dawayya ya gayyace mu fim wani gida, ba tare da izinin mai gidan ba, sanadiyyar haka sai da muka je gidan yari na tsahon wata guda mu biyar, da ni da Falalu Dorayi, da Jibrin S. Fage, da Mansoor Sadik, da shi Ali Dawayya, da kuma Wanda ya yi sanadiyyar kai mu gidan, ba zan taba mantawa da wannan ib’tila’in ba.

A cikin jerin fina-finan ka wanne ya fi baka wahala, kuma wanne ka fi so?

Na sha wahala a fim din Badali, har suma na yi ana aiki, sannan na sha wuya a fim din Karen Bana, na sha wuya a fim din Garinmu Da Nisa. Kazalika ina son fim din Sa’a Dai, da fim din Tarkon Kauna Da Ahalul Kitab, da Karangiya, da Hawan Dare.

Ana kiran ka da Asase Ko za ka fada mana yadda ka samo sunan?

Sunan ya samo a sali ne daga ‘Asasination’ mutun me kashe mutane, amma a fim, daga ‘Asasintion’ ya koma Asase.
Sau tari kana fitowa mugu a fim yaranka ko mutanen gari a gaske ba sa gudunKa kuwa?
Na samu wannan matsalolin da yawa, na samu a masu ziyara, na samu a asibiti na samu a gidan gaisuwa, na samu a kasuwa, an ganni an fashe da kuka, an ganni an gudu, ba zan manta ba akwai wani lokaci mun je biki Kaduna da ni da abokan sana’ata, an sauke mu a wani otel a cikin kawayen amarya da suke kawo mana abinci wata da ta ganni da ta zubar da kayan abincin ta manne da gudu har aka gama bikin ban kara ganin ta ba.

Wace shawara Za ka bai wa masu son shiga sana’ar fim din hausa a yanzu?

Kai kokari ka santa kafin ka shige ta don kar ka shigo ka zo ka ce wani ya cuce ka don Allah ma ya ce kasanni kafin ka bauta min.
Shin za ka iya barin diyarka ta fito a fim
Na ma saka ta, kuma ina kan sawa, idan har baza ka iya sa danka ko ‘yarka ba, to kai ma ya kamata ka fita daga ciki.
A jerin jarumai maza da mata su waye gwanayenka
Jarumina Bashir na yaya (Dan Magori) da marigayi Alh. Rabilu Musa (Dan ibro) jarumata kuma, marigayya Hafsat Sharada (Yaya Me Aya) da marigayya Hauwa Ali dodo, wato (Biba) Ubangiji Allah ya kai rahama kabarinsu, Allahumma Ameen.
Zaka iya auren jarumar da ta yi Suna a fim
Da gudu ma, sai dai in ban samu wacce ta dace da ni ba, kowane mutum yana rayuwa ne akan tarbiyar sa kuma duk abin da kake kyama to kaurace masa akeyi
Shin ko Kana da sha’awar fara ba da umarni (Directing) naka na kanka
Ina dai shi’awar daukar nayin fim ‘Producing.’ kuma ina yi ina yin manajan shiri, ni abin da na dauki ba da umarni ‘Directing,’ aiki ne na masu hankali na masu nutusuwa, wadan da ba su da saurin fushi wanda za su iya sarrafa kowa shi ya sa ni zuciyata ba za ta iya ba.
Mun gode sosai da lokacin da ka bamu
Ni ma na gode sosai Allah ya saka da mafificin Alkhairi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button